✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An rufe cocina 3 kan damun jama’a da kara

Gwamnatin Jihar Ogun ta rufe wasu cocina uku kan damun jama'ar yankunansu da kara.

Gwamnatin Jihar Ogun ta rufe wasu cocina uku saboda suna damun jama’ar yankunansu da kara.

Da yake rufe cocinan a birnin Ibadan, mashawarcin gwamnan jihar kan muhalli, Farook Akintunde, ya ce an sha gargadin aike wa cocinan takardar gargadi da kuma zaman tattaunawa da cewa su daina yadda suke hana jama’a sakat, amma suka ki.

Akintunde ya ci an samu cocin Christ Apostolic da ke yanin Gbogunmi yana amfani da manyan sifiku a lokacin ibadar yamma da na tssakar dare, wanda karar sififkun ke hana jama’ar unguwar sukuni.

“Jama’ar unguwar sun shain yin korafi har suka rubuta wa gwamnati takardar koke cewa karar da ke fitowa daga cocin na cutar da lafiyarsu.

“Duk kokarinmu na ganin shugabannin cocin sun daina ya ci tura, amma babu gwamnatin da za ta zura ido ana cutar da lafiyar al’ummar da take shgabanta,” in ji Akintunde.

Daga nan sai ya yi gargadi wuaren ibada da su daina damun jama’a da kara, saboda gwamnati ba za ta yi kasa a gwiwa wajen rufe duk wanda ya saba dokar ba.

Hakazalika ya yi kira ga masu neman hana ma’aikata zartar da aikinsu cewa su daina ko kuma su dandana kudarsu.