✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Bata-gari sun fasa gidan Yakubu Dogara

Sun karya dokar hana fita suka rika fasa gine-ginen gwamnati suna neman kayan tallafin COVID-19

A safiyar Lahadi wasu bata-gari suka fasa gidan tsohon kakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara da ke garin Jos, Jihar Filato.

Jaridar Punch ta rawaito cewa bata-garin sun karya dokar hana fita da gwamnatin jihar ta saka, inda suka shiga fasa gine-ginen gwamnati domin neman kayan tallafin COVID-19.

“Sun fasa gidan tsohon Shugaban Majalisar Waiklai, Dogara, sun farmaki duk wanda suka samu a gidan, ciki har da dan uwansa.

“Sun kwashe kayayyaki da dama daga ciki har da kayan laturoni, kujeru da sauran kayan amfanin gida”, inji wani ganau.

Wanda lamarin ya faru a kan idonsa, ya shaida wa manema labarai cewa-bata garin sun fasa gidan Dogara ne da misalin karfe 9 na safe.

Sai dai jami’an tsaro sun tarwatsa gungun bata-garin ta hanyar yin harbi a iska.