✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Real Madrid da City sun fito ‘semi-final’ a gasar kofin Zakarun Turai

City za ta kara da PSG yayin da Real Madrid za ta gwabza da Chelsea a matakin kusa da na karshe na gasar.

Real Madrid ta samu nasarar kaiwa zagayen daf da na karshe a gasar cin kofin Zakarun Turai, bayan wasan da ta fafata a daren ranar Laraba tare da Livepool a filin wasa na Anfield da ke Ingila.

Wannan nasara da Real Madrid ta samu na zuwa ne duk da cewa an tashi wasan babu ci tsakaninta da Liverpool.

Galabar da Madrid ta yi a kan Liverpool da ci 3-1 a Spain yayin wasan da suka fatata a zagaye na farko na matakin kwata final a makon jiya ce ta yi tasiri wajen samun nasarar zarcewa matakin daf da na karshe na gasar wato semi final.

Haka kuma, Manchester ta samu nasarar kai wa matakin daf da na karshe a gasar bayan ta lallasa Dortmund da ci 2-1 gida da waje.

Yayin haduwarsu a daren na Laraba, City ce ta sake samun nasara a kan Dortmund da ci 2-1, kamar dai yadda ta doke ta yayin fafatawar da suka yi a zagayen farko na wasan a matakin daf da na biyu karshe, kwata final.

Kamar dai yadda mahukunta gasar cin kofin Zakarun Turan suka tsara, a yanzu Manchester City za ta kara da PSG yayin da Real Madrid za ta gwabza da Chelsea a matakin kusa da na karshe na gasar.