✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

1443 Hijiriyya: Ganduje ya ba da hutu ranar Litinin

Gwamnan ya bukaci jama'a da roka wa Najeriya zaman lafiya.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano ya ayyana ranar Litinin, 1 ga Muharram, 1443 bayan Hijira, wadda ta yi daidai da 9 ga Agusta, 2021, a matsayin ranar hutu a jihar.

Sanarwar da Kwamishinan Yada Labaran Jihar, Muhammad Garba ya fitar ta ce an ba da hutun domin bikin ranar sabuwar shekarar Musulunci ta 1443 bayan Hijira.

  1. Labarin rataye kai ya sa malamai nadama a Zariya
  2. DSS na binciken jami’anta kan cin zarafin dan jarida

Gwamnan ya bukaci ma’aikata da su yi amfani da ranar da babu aiki don yin addu’a ga kasa don kubutar da ita daga matsalolin tsaro.

Ya kuma taya Musulmi murnar shigowar sabuwar shekarar Musuluncin, tare da yin godiya ga Allah Madaukakin Sarki.

Sanarwar ta kara neman goyon baya da hadin kai na jama’a ga gwamnati yayin da take kokari don inganta muradansu duk da irin kalubalen da kasar ke fuskanta.

Tuni jihohi da dama a Najeriya suka shiga ba da hutu domin nuna murnar shigowar sabuwar shekarar Musulunci.