✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

1443: Jihar Osun ta ayyana hutun sabuwar shekarar Musulunci

Gwamnan ya kuma rki al'ummar Jihar da su yi wa Jihar addu'a a lokacin.

Gwamnan Jihar Osun, Adegboyega Oyetola ya ayyana Litinin mai zuwa a matsayin ranar hutu domin murnar zagayowar sabuwar shekarar Musulunci ta 1443.

Kwamishinan Harkokin Cikin Gida na Jihar, Tajuddeen Lawal ne ya sanar da haka ranar Juma’a.

A cewarsa, Gwamnan ya kuma yi kira ga al’ummar Jihar da su yi amfani da lokacin wajen yin addu’ar ci gaban Jihar da ma Najeriya baki daya.

A wani labarin kuma, Kungiyar ’Yan Jarida Musulmai ta Najeriya (MMPN) ta yi kira ga sauran Jihohin Najeriya da su bi sahun Jihar ta Osun wajen ayyana ranar ta daya ga watan Almuharram a matsayin ranar hutu.

Shugaban kungiyar na kasa, Alhaji Abdur-Rahman Balogun ne ya yi kiran inda ya ce yin hakan yin adalci ne da tabbatar da daidaito ga al’ummar kasa.

Ya kuma yaba wa Gwamnonin da suka ayyana ranar a matsayin hutu, musamman a Arewacin Najeriya da kuma Jihohin Osun da Oyo a Kudu maso Yamma, inda ya yi kira ga sauran Jihohi da su yi koyi da su.

Balogun ya kuma yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ita ma amince da ranar a hukumance domin ba Musulmai dama kamar yadda ake ba takwarorinsu Kiristoci a ranar daya ga watan Janairun kowacce sabuwar shekarar Miladiyya.

Ranar daya ga watan na Almuharram dai ita ce ranar farko a shekarar Musulunci, kuma a bana za a shiga shekara ta 1443.

An fara lissafin shekarar ne tun lokacin da Annabi Muhammad (S.A.W.) ya yi Hijira daga birnin Makkah zuwa Madina, wadanda a yanzu suke a kasar Saudiyya.