✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

1443: Talata ce 1 ga watan sabuwar shekara – Sarkin Musulmi

Hakan dai ya biyo bayan rashin ganin jinjirin wata ranar Lahadi.

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya ayyana ranar Talata a matsayin ranar daya ga watan Almuharram na sabuwar shekarar Musulunci ta 1443 bayan Hijira.

Sarkin, wanda kuma shine shugagan Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci a Najeriya (NSCIA), ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwar da ya fitar da yammacin ranar Lahadi a Abuja.

Sanarwar, wace Daraktan Mulki na majalisar, Akitek Zubairu Haruna Usman-Ugwu ya sanya wa hannu, ta ce hakan na nufin ranar Litinin, tara ga watan Agustan 2021 ita ce za ta kasance 30 ga watan Zhul-Hijjah na shekarar 1442.

“Bayan la’akari da shawarwarin Kwamitin Duban Wata, Mai Alfarma Sarkin Musulmi kuma shugaban Majalisar Koli ta NSCIA ya ayyana ranar Talata, 10 ga watan Agustan 2021 a matsayin daya ga watan Almuharram na shekarar 1443 bayan Hijira,” inji Usman-Ugwu.

Sarkin Musulmin ya kuma taya dukkan al’ummar Musulmin Najeriya murnar sabuwar shekarar.

Tun da farko dai an umarce Musulmi ne su fara duban jinjirin watan na Almuharram daga ranar Lahadi, takwas ga watan Agustan 2021.

Watan Almuharram dai shi ne wata na farko a shekarar Musulunci, wacce aka fara lissafinta bayan hijirar Annabi Muhammad (S.A.W) daga Makkah zuwa Madina.