✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kashi 71 na likitoci 280 da muke biyan albashi na bogi ne —Matawalle

Muna biyan albashin likitoci 280 amma mun gano cewa likitoci 81 kacal ne na hakika.

Gwamnan Jihar Zamfara, Muhammad Bello Matawalle, ya ce gwamnatinsa ta gano sunayen likitocin bogi kimanin 199, wadanda ake biyan albashi a jihar.

Gwamna Matawalle na wannan jawabi ne a wani taron manema labarai a gidansa da ke Karamar Hukumar Maradun.

Matakin na zuwa ne a dai-dai lokacin da ake kokawa game da tsaikon da aka samu wajen biyan albashi ma’aikatan lafiyar jihar, lamarin da Gwamna Matawalle ya ce cuwa-cuwar da suka bankado ce sila amma tuni sun sauke nauyin duk wani albashi na watannin Nuwamba da Disamba.

A cewar gwamnan yayin da gwamnatin jihar ke biyan likitoci 280 albashi a jihar a duk wata, ta gano cewa likitoci 81 ne kawai ke aiki a jihar.

“Muna biyan albashin likitoci 280 amma mun gano cewa likitoci 81 kacal ne na hakika.”

Gwamnan ya kara da cewa tuni ya zanta da Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC) domin gano wadannan likitoci 199, da suka kwashe tsawon lokaci suna karbar albashi alhalin ba sa yi wa gwamnatin jihar aiki.

Ya kuma ce akwai bukatar a gano wadanda ke da hannu a wannan cuwa-cuwa.

Matawalle ya ce an gano wadannan sunaye ne sakamakon aikin tantance ma’aikata da gwamnatin jihar ke gudanarwa karkashin Ofishin Shugaban Ma’aikata na jihar, a wani bangare na kokarin da gwamnatin ke yi na fara aiwatar da tsarin biyan albashi mafi karanci na N30,000.

‘Ba za mu rage ma’aikata ba’

Gwamna Matawalle ya ba da tabbacin cewa gwamnatinsa ba za ta rage ma’aikata ba kan batun aiwatar da mafi karancin albashin.

“Ba zan kori ko wane ma’aikaci ba da yake yi wa gwamnati aiki.

“Maganar gaskiya ma na gina gidaje 450 domin ma’aikatan jihar nan kuma zan mika gidajen garesu ranar Lahadi.

­“Amma za mu tsaftace ma’aikatunmu bisa tafarkin doka domin bada damar fara biyan N30,000 a matsayin albashi mafi karanci,” in ji shi.

Gwamna Matawalle ya kuma ce gwamnatinsa za ta rubanya kokarin da take yi domin inganta harkar kiwon lafiya ga duk ’yan jihar, matukar aka sake zabensa a karo na biyu.

Ko a shekarar 2019 ma, Gwamnatin Zamfara ta ce za ta gurfanar da ma’aikatan da ta gano suna karbar albashi fiye da daya a gaban kotu, bayan ta kaddamar da bincike domin gano ma’aikatan bogi.

Matsalar likitocin bogi ta dade ana fama da ita a matakin jihohi da Gwamnatin Tarayya.

Masana sun alakanta yadda ake samun zirarewar kudaden gwamnati ga matsalar ma’aikatan bogi.

‘Tinubu zai magance matsalar tsaro’

Dangane da batun tsaro, Gwamnan ya ce dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya yi alkawarin kafa matatar zinare a Jihar Zamfara.

Ya ce wannan wani mataki ne da Tinubun zai dauka a kokarin kawo karshen matsalar tsaro a jihar.

Gwamnan ya ce, “Lokacin da na zauna da dan takararmu na Shugaban Kasa, sai na ce masa matsalarmu a Jihar Zamfara ita ce ta ’yan fashi da makami; wane tanadi ka yi domin kawo karshen wannan barazana?

“Ya ce (Tinubu) ya ce idan suka kafa matatar zinare a jihar, wadanda za su dora wa nauyin aikin ne za su tsara yadda za a kare wadannan albarkatu kuma na gamsu da bayanansa.”