✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

2022: Shugaban Karamar Hukuma ya gabatar da kasafin kudin N4.7bn a Kaduna

Ya ce majalisarsa na hankoron tara Naira biliyan 1.4 a matsayin kudaden shiga.

Shugaban  Karamar Hukumar Kaduna ta Arewa da ke Jihar Kaduna, Mukhtar Baloni, ya gabatar da Naira biliyan 4.7 a matsayin kasafin kudin 2022 a gaban Majalisar Karamar Hukumar.

Shugaban, yayin da yake gabatar da kasafin, ya ce majalisarsa na hankoron tara Naira biliyan 1.4 a matsayin kudaden shiga na cikin gida a shekarar ta 2022.

Ya ce, “An tsara kasafin kudin ne daidai da bukatun mutanenmu, kuma bangarorin da suka fi samun kaso mafi tsoka sune na bunkasa rayuwar jama’a da ilimi da lafiya da kuma tsaro.

“Wadannan sune bangarorin da kasafin zai fi mayar da hankali a kansu,” inji shi.

A cewar Shugaban, kafin a kai ga gabatar da kasafin, sai da Karamar Hukumar ta shirya taruka da masu ruwa da tsaki daban-daban domin jin bukatun mutane na kai tsaye.

Baloni ya kuma ce kasafin zai mayar da hankali sosai ga masu karamin karfi da kuma bukatunsu.

Ya kuma ce Karamar Hukumar ta sanya bai wa dalibai ’yan asalin cikinta da ke karatu a Jami’ar Jihar Kaduna (KASU) tallafi da kuma kirkiro da shirin koya wa matasa sana’o’i don a rage zaman kashe wando.

Da yake nasa jawabin, Kakakin Karamar Hukumar, kuma Kansila mai wakiltar mazabar Hayin Banki, Umar Iliyasu, ya yaba wa Shugaban tare da yin alkawarin ba shi dukkan goyon bayan da yake bukata.