✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

2023: An nada tsohon Mataimakin Gwamnan Kano shugaban yakin neman zaben Osinbajo

An dai tabbatar da nadin nasa ne tare da wasu shugabannin tafiyar yayin wani taro a Kano.

An nada tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Farfesa Hafizu Abubakar, a matsayin Shugaban Kungiyar Yakin Neman Zaben Yemi Osinbajo (OSO) a matsayin Shugaban Kasa a 2023.

An dai tabbatar da nadin nasa ne tare da wasu shugabannin tafiyar yayin wani taron kungiyar da ya gudana a Kano ranar Asabar.

Farfesa Hafizu dai shi ne Mataimakin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje daga shekarar 2015 zuwa 2018.

Taron dai ya samu halartar kungiyoyin magoya bayan Mataimakin Shugaban Kasar da suka fito daga sassa daban-daban na Najeriya.

Da yake jawabi yayin taron, Daraktan Tsare-tsare na kungiyar, Bashir Suwaid, ya ce akalla kungiyoyin da ke goyon bayan Osinbajo sama da 45 ne suka halarci taron.

Kazalika, taron ya kuma zabi shugabanni daga dukkan shiyyoyin siyasa guda shida na kasar nan.

“Akwai kungiyoyi 45 da suka zo daga sassa daban-daban na kasar nan domin kaddamar da jagororin kungiyar OSO a hukumance, inda tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Farfesa Hafizu Abubakar, a matsayin jagora,” inji Bashir Suwaid.

Sauran mukaman jagororin kungiyar sun hada da Daraktan Tsare-tsare da Mai ba da Shawara a Bangaren Shari’a da Daraktan Kudi da na Wayar da Kan Jama’a da na Mulki da kuma na Yada Labarai da dai sauransu.