✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

2023: APC ta nemi Atiku da Saraki su dawo cikinta

Jam'iyyar APC na neman Atiku da sauran manyan mutane da suka fice daga cikinta da su dawo kafin zaben 2023.

Jam’iyyar APC ta yi kira ga tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar da Gwamnan Sokoto Aminu Tambuwal da tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki da Gwamnan Benue Samuel Ortom, da suka fice daga cikinta da sake dawowa.

APC ta kirayi manyan mutanen ne bayan sake dawowa cikinta daga jam’iyyar PDP gabanin zaben 2023 da Sanata Barnabas Gemade da tsohon Kakakin Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara suka yi.

Mataimakin Sakataren Watsa Labaran APC na Kasa, Yekini Nabena ya sanar da shirin jam’iyyar na sake karbar masu neman dawowa cikinta.

“Muna tabbatar wa duk ‘yan APC da suka bar ta saboda wasu dalilai da ke neman sake dawowa cikinta, da kuma shirinta na yi wa kanta gyare-gyare domin cimma manufofinmu na hidimta wa kasar.

“Abu mai dadi ne ganin magoya bayan jam’iyyar …sun fara gamsuwa da yunkurin sasancin kwamitin Buni kuma suna goyon bayan kwamitin.

“Muna kira ga dukkan masu goyon bayan jam’iyya da shugabanninta da ‘ya’yanta da su goyi bayan shugabannin riko da ke sasanta bangarorin jam’iyyar.

“Aikin tabbatar da hadin kai da dunkulewar jam’iyyar aikinmu ne baki daya”, inji sanarwar.