✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

2023: APC ta zabi Lalong a matsayin shugaban yakin zaben Tinubu

APC ta ce Lalong na da hikimar da zai iya jan ragamar yakin neman zaben Tinubu a 2023.

Jam’iyyar APC ta tabbatar da Gwamnan Jihar Filato kuma Shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewa, Simon Lalong a matsayin Darakta-Janar na yakin neman zaben Bola Tinubu a matsayin Shugaban Kasa.

Shugaban jam’iyyar na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, ne ya bayyana hakan ga manema labarai na Fadar Shugaban Kasa ranar Alhamis, jim kadan bayan ganawa da Shugaba Muhammadu Buhari a Abuja.

Ya ce, “Mun zo nan ne domin ganin Shugaban Kasa don yi masa bayani da kuma neman amincewarsa kan tsare-tsaren da muke yi dangane da yakin neman zabe.

“Kuma da zarar mun samu yardarsa, muna da niyyar yin bayani. Muna tare da Shugaban Kasa da kuma daidaikun mutanen da za su taka rawa daban-daban a yakin neman zaben 2023.

“Darakta-Janar na kamfen yana zaune a dama na a nan. Gwamna Simon Lalong na Jihar Filato.

“Kakakin yakin neman zabenmu shi ne Festus Keyamo. Mataimakiyar kakakin ita ce Hannatu Musawa. Wannan shi ne abin da muka zo don tattaunawa da Shugaban Kasa,” inji Abdullahi Adamu.

Ya kuma ce zaben Lalong ya ta’allaka ne kan yadda ya taka muhimmiyar rawa wajen nasarar takarar Tinubu da Shettima.

“Shugabancin jam’iyya ya san cewa zai iya tafiyar da harkokin yakin neman zabe,” inji shi.