✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

2023: Ba mu da dan takara a Najeriya —Birtaniya 

Birtaniya ta ce za ta yi aiki da duk dan takarar shugaban kasa da ya shiga zaben 2023 da ke karatowa.

Gwamnatin Birtaniya ta ce babu wani dan takarar shguaban kasa da take goyon baya a zaben Najeriya na 2023.

Jakadiyar Birtaniya a Najeriya, Catriona Liang, ce ta sanar da hakan bayan wata ganawar sirri da Kwamitin Gudanarwa na Jam’iyyar APC na Kasa a Abuja ranar Laraba.

“Babu wani dan takara da Birtaniya ta fi so, mun fi damuwa mu ga an yi sahihin zabe; Amma za mu yi aiki da duk dan takarar shugaban kasar da ya fito zaben,” in ji Misis Liang.

Jakadiyar ta kuma jaddada amincewar gwamnatin Birtaniya da kudurin Najeriya na tabbatar da  dorewar tsarin dimokuradiyya da yadda Shugaba Buhari ya lashi takobin gudanar da zabuka masu inganci da kwanciyar hankali.

A cewarta, “Birtaniya da Najeriya na da kyakkyawar alaka, kuma muna son ganin Najeriya ta yi nasara da wanzuwar dimokuradiyya a cikinta.”

A watan Fabrairun shekarar 2023 ne Najeriya za ta gudanar da zaben shugaban kasa, wanda shi ne karo na bakwai tun bayan dawowar kasar kan tsarin dimokuradiyya a shekarar 1999.