✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

2023: Ba ni da dan takarar shugaban kasa —Buhari

Shugaban ya bayyana hakan ne ranar Litinin a taronsa da gwamnonin jam'iyar na Arewacin Najeriya da aka yi a Abuja.

Shugaba Buhari ya ce ba shi da wani dan takarar shugaban kasa da yake goyon baya, kuma babu wani da ya bayyana a matsayin wanda yake so ya gaje shi gabanin zaben fidda gwanin kujerar a jami’iyar ta APC ranar Talata.

Shugaban ya bayyana hakan ne ranar Litinin a taronsa da gwamnonin jam’iyar na Arewacin Najeriya da aka yi a Abuja.

Buhari ya kuma kauda shakkun matsayarsa kan wanda zai gaje shi a zaben 2023 a jam’iyar, in da ya ce babu wani dan takarar da zabar shi a zaben fidda gwanin ya zamo tilas ga kowa.

Haka kuma, ya ce jam’iyar da mambobinta na da muhimmancin gaske da kuma ba su muhimmaci a cikinta.

A wata sanarwa da ya fitar ta hannun kakakinsa Garba Shehu ya ce babu wani kulli a zuciyarsa da abin da yake, kuma suma gwamnonin su sanya haka a ransu.

“An zabe ku kamar yadda aka zabe ni, zuciyarku ta zama fes kamar tawa, Allah ne Ya ba mu dana don haka ba mu da wani hujjar yin korafi. Mu shirya daukar sakamakon da ya yi mana dadi ko akasinsa.

“Mu bar Daliget su yi aikinsu”, in ji Buhari.
Tun da fari dai Shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewa, Simon Lalong da Gwamna Atiku Bagudu da ke Shugabantar Kungiyar Gwamnonin APC sun sake tabbatar da matsayar gwamnonin Arewan cewa dole dan takarar shugaban kasan APC ya fito daga yankin Kudancin kasar nan.