✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

2023: Ba za mu ba Kwankwaso tikitin takarar Shugaban Kasa kai-tsaye ba — NNPP

Jam’iyyar NNPP ta ce tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da ya ba ta tabbacin dawowa cikinta zai iya neman tsayawa takarar Shugaban…

Jam’iyyar NNPP ta ce tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da ya ba ta tabbacin dawowa cikinta zai iya neman tsayawa takarar Shugaban Kasa a jam’iyyar a zabe mai zuwa amma ba zai samu tikitin jam’iyyar kai-tsaye ba.

Sakataren Jam’iyyar NNPP na Kasa mai barin gado, Ambasada Agbo Gilbert Major ya bayyana wa taron Kwamitin Zartarwar Jam’iyyar a ranar Talata cewa Sanata Kwankwaso zai dawo jam’iyyar tare da tafiyar siyasara ta TNM da kuma magoya bayansa.

“Na san ’yan Najeriya na ta hasashe, to, ina tabbatar muku cewa mun yi nisa a tattaunawa da Kwankwaso, har mun kusa kammalawa. Nan da ’yan kwanaki za mu sanar da su inda aka kwana. Amma tabbas saura kiris Kwankwaso ya dawo NNPP,” inji shi.

Major, ya shaida wa taron da jam’iyyar ta shirya domin tunkarar zaben 2023 cewa Sanata Kwankwaso ya ba da tabbacin cewa zai kasance dan jam’iyya mai biyayya tare da bin dokokinta kamar kowane dan jam’iyya.

Babu takarar kai-tsaye

Sai dai Agbo ya ce NNPP ba za ta ba wa tsohon Ministan Tsaron tikitin tsayawa takarar Shugaban Kasa kai-tsaye ba, za ta ba wa sauran masu sha’awa damar gwada farin jininsu.

“Babu batun ba Kwankwaso tikitin takarar Shugaban Kasa kai-tsaye, kuma ya shaida mana cewa ba ya kaunar a dauka cewa ya shigo NNPP ne domin kawai ya samu tikitin takara.

“Mun ba sauran masu neman takara kwarin gwiwa su fito su gwada farin jininsu da kuma amfani da ’yancinsu na tsayawa takara da na jama’a na zaben wanda suke so,” inji Agbo Major.

Kasa da mako biyu ke nan da tsohon Gwamnan Jihar Kanon ya assasa tafiyar siyasa ta TNM wadda ya jagoranci taron kaddamar da ita a Abuja.

Kawo yanzu dai babu wani martani da daga bangaren TNM ko Kwankwaso game da sauya sheka zuwa NNPP.

A kwanakin baya Aminiya ta kawo rahoton cewa Jam’iyyar APC mai mulki na zawarcin Kwankwaso ya sake dawo cikinta kafin zaben 2023.

Wadansu makusantan Kwankwaso sun ce tattaunawa a tsakanin bangarorin ta yi nisa, amma ba a cim ma matsaya a kan batun ba, wanda ake zaton a karkashinsa, Kwankwaso zai zama dan takarar Mataimakin Shugaban Kasa ga Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo.

Kwanaki kadan bayan hakan ne tsohon Ministan Tsaron da abokan siyasarsa suka kaddamar da tafiyar siyasa ta TNM, wadda ake sa ran za su yi amfani da ita domin yin hadin gwiwa da wata jam’iyya don kaiwa ga manufarsa ta tsayawa takarar Shugaban Kasa a zaben 2023.

Sai dai a yayin kaddamar da TNM, Kwankwaso ya bayyana cewa APC da jam’iyyarsa ta PDP ba su ne mafita ga al’ummar Najeriya ba.