✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

2023: Babu abin da zai hana mai nadin sarki zama sarki —Tinubu

Babu abin da zai hana mai nadin sarkin zama sarki.

Asiwaju Bola Tinubu, jagora a jam’iyyar APC mai mulkin kasar, ya sanar cewa babu abin da zai hana mai nadin sarkin zama sarki.

Wannan dai na zuwa ne a yayin da ya sanar da Shugaba Muhammadu Buhari kudirinsa na neman takarar kujerar shugaban kasa a babban zaben 2023 da ke tafe.

Tinubu ya bayan na hakan ne yayin ganawa da manema labarai na Fadar Shugaban Kasa ta Aso Rock da ke Abuja, babban birnin kasa.

A cewar Tinubu “na shaida wa Shugaba Buhari aniyata, ban ji abun da ba shi na yi tsammanin ji daga gare shi ba, ya karfafa min gwiwa kamar yadda dimokuradiyya ta ba ni dama, amma har yanzu ban sanar da jama’ar Najeriya ba tukunna, ina ci gaba da tuntuba.

Da yake bayyana martanin Buhari, Tinubu ya ce “Tuntuni nake fatan zama shugaban kasa a tsawon rayuwata, don haka me ya sa zan yi tsammanin jin abun da ya saba da wannan daga wajen shi, tsari muke yi da dimokuradiyya, don haka dole mu tafi a kan haka”, in ji shi.

Tinubu dai na daya daga cikin jiga-jigan da suka tsaya tsayin-daka wajen ganin Buhari ya samu nasara a zaben 2015, lamarin da ya sanya yake bugun gaba zai gaji kujerarsa a zaben 2023.

A yau Litinin ce dai Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Tinubu, wanda da isarsa suka shiga ganawar sirri.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, ganawar ba za ta rasa nasaba da jan kafar da ake yi ba wajen tsayar da ranar da za a gudanar da babban taron jam’iyyar APC, wanda a nan ne za ta zabi shugabanninta.

Tun gabanin yanzu ta bayyana cewa Tinubu na daga cikin jiga-jigan jam’iyyar APC da ke hankoron samun tikitin takarar kujerar shugaban kasa a babban zaben kasar na 2023.

Dabdalar babban taron jam’iyyar APC

A Juma’ar da ta gabata ce Shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewa, Gwamna Simon Bako Lalong na Jihar Filato, ya ganawa da Shugaba Buhari a kan batun babban taron jam’iyyar.

Jim kadan bayan ganawar ta su ce kuma Shugaban Kwamitin Riko na jam’iyyar APC na kasa, Gwamna Mai Mlaa Buni na Jihar Yobe, shi me ya gana da shugaban kasar kan babban taron wanda shi jam’iyyar ta sanya gaba a halin yanzu.

Kazalika, a wata hira ta musamman da ya yi da Gidan Talabijin na Kasa NTA, Shugaba Buhari ya gargadi jam’iyyar a kan ta yi taka tsan-tsan wajen warware duk wasu matsalolinta don gudun kada wata jam’iyyar adawa ta yi mata mahangurbar kwace madafan iko a zaben 2023.

Da dama dai daga cikin ’ya’yan jam’iyyar ta APC na ci gaba da bayyana damuwa kan makomar jam’iyyar, inda ake ta yi wa shugabanninta matsin lamba dangane da jan kafar da ake yi na fara shirye-shiryen babban taronta da ake sa ran gudanar da shi a watan Fabrairu.