✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

2023: Babu Sanata Ahmed Lawan a sunayen ’yan takara —INEC

An rika kai ruwa rana tun bayan da Bashir Machina ya zama dan takarar Sanatan Yobe ta Arewa.

Babu sunan Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmed Lawan a cikin jerin sunayen ’yan takarar da za su fafata a Babban Zaben na 2023.

INEC ta fitar da jerin sunayen ne a ranar Talata, 20 ga watan Satumban 2022, inda ta ce jerin na kunshe ne da sunayen ’yan takara daga jam’iyyu 18.

Sai dai a cikin jerin sunayen, babu wani dan takara da INEC ta nuna a matsayin tabbataccen dan takarar kujerar Sanatan Yobe ta Arewa.

Aminiya ta ruwaito yadda aka rika kai ruwa rana a jam’iyyar APC tun bayan da Bashir Machina ya zama zakara na zaben fidda gwanin takarar Sanatan Yobe ta Arewa da aka gudanar, wanda wakilan Hukumar Zabe ta Kasa INEC suka shaida.

Lawan wanda yana daya daga cikin jiga-jigan ’yan siyasa da suka gwada sa’arsu ta neman tikitin takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, ya sha kaye a hannun tsohon gwamnan Jihar Legas, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

Sai dai bayan shan kasa ne Sanata Lawan ya nemi yi wa tikitin takarar Sanatan Yobe ta Arewa hawan kawara a kokarinsa na kwace nasarar da Bashir Machina ya yi.

INEC dai ta fitar da jerin sunayen ’yan takarar Shugaban Kasa da Majalisar Dattawa da kuma na Majalisar Wakilai na dukkan jam’iyyun kasar da za su fafata a zabukan 2023.

An wallafa jerin sunayen na ’yan takara daga dukkan mazabun kasar a shafin intanet na INEC.

Za a gudanar da zaben Shugaban Kasa da na Majalisun Dokokin Tarayya a ranar 25 ga watan Fabrairun 2023 sai na gwamnonin da Majalisun Dokokin Jihohi a ranar 11 ga watan Maris din 2023.

A jerin sunayen, akwai ’yan takarar Shugaban Kasa da mataimakansu 18 daga jam’iyyu daban-daban, sai kuma ’yan takarar Majalisun Tarayya daga jihohi 36 da babban birnin kasar Abuja, karkashin jam’iyyu daban-daban.

Baya ga sunayen ’yan takarar da ta wallafa, INEC ta kuma bayyana jinsi da shekaru da matakin ilimi na kowane dan takara.

‘Yan takarar shugaban kasa da aka fitar da jerin sunayen nasu sun hada da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC; Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP; Peter Obi na Jam’iyyar LP, Rabi’u Musa Kwankwaso na Jam’iyyar NNPP da Adebayo Adewole na Jam’iyyar SDP da sauransu.

Sai dai kamar yadda kotu ta ba da umarni, INEC ta fitar da sunan tsohon Ministan Harkokin Neja Delta, Godswill Akpabio a matsayin dan takarar Sanatan APC na shiyyar Akwa Ibom ta Arewa maso Yamma.