✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

2023: Bayan shekara 23 a Majalisa, Ahmad Lawan ya yi biyu babu

Bashir Machina Sheriff ya ce maganar ya janye wa Ahmad Lawan ba ta ma taso ba, domin ya dade yana burin zama Sanata mai wakiltar…

Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan, na fuskantar barazana dangane da yunkurinsa na komawa majalisar a zaben 2023.

Wannan na zuwa ne bayan mutumin da ya lashe zaben dan dakarar Sanata mai wakiltar Yobe ta Arewa a Jami’yyar APC, Bashir Sheriff Machina, ya lashi takobin cewa ba zai janye ba wa Shugaban Majalisar Dattawan ba.

A wata hira ta musamman da wakilinmu ya yi da shi ranar Litinin da dare, Bashir Machina ya ce, “Har yanzu ni ne dan takara, ban janye wa kowa ba kuma ba zan janye ba”.

Wannan sabuwar dambarwa ta taso ne bayan Sanata Ahmad Lawan ya fadi zaben dan takarar shugaban kasa a Jam’iyyar APC.

Bayan haka ne masu ruwa da tsaki na Jam’iyyar APC reshen Jihar Yobe suka fara yunkurin ganin Bashir ya janye mishi, shi kuma ya ce ba za ta sabu ba.

Dan takarar ya shaida wa wakilinmu cewa maganar ya janye wa wani ba ta ma taso ba.

Ya bayyana cewa tsayawa ya yi neman takara, daliget suka yi mishi ruwan kuri’u domin ya zama Sanata mai wakiltar Yobe ta Arewa a Majalisar Dattawa a 2023.

Ya ce, “Abin da na sani shi ne tsayawa neman takarar Sanata mai wakiltar Yobe ta Arewa na yi kuma na yi nasara.

“An tabbatar da ni a matsayin wanda ya ci zaben babu hamayya saboda ni ne kadai na cancanta bayan an soke sauran masu neman takarar.”

Mastin lamba ga Bashir Machina

Ya ce, “Mutane da yawa sun zo suna  neman in janye, amma ba zan janye ba, Insha Allah,” in ji shi.

Ya ci gaba da cewa a shirye yake ya fafata da ’yan takarar sauran jam’iyyu a zaben ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023, da ke kara matsowa.

Wani dan Jam’iyyar APC kuma makusancin Bashir Machina, Hussaini Mohammed Isa, ya ce dan takarar na fuskantar matsin lamba daga wasu kusoshin jam’iyyar cewa ya janye wa Ahmad Lawan.

Sai dai ya soki yunkurin, inda ya ce
Machina ya samu tikitin takarar ne da guminsa.

Ahmad Lawan ne ya fi dacewa

A nasu bangaren, magoya bayan Ahmad Lawan, sun ce shi suke so ya ci gaba da wakiltar yankin a Majalisar Dattawa.

A cewar Saleh Mohammed, har yanzu babu wanda ya kai Ahmad Ibrahim Lawan nagarta a cikin duk Sanatocin da suka fito daga yankin.

Shekara 23 ke nan da Ahmad Lawan yake wakiltar Jihar Yobe a Majalisar Dokoki ta Kasa, tun daga shekarar 1999 da Najeriya ta koma mulkin dimokuradiyya.

Kawo yanzu, shekarunsa 15 yana wakiltar Yobe ta Arewa a Majalisar Dattawa, tun daga shekarar 2007.

Kafin nan kuma ya kasance dan Majalisar Wakilai tun daga 1999.