✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

2023: Buhari ya sake ganawa da gwamnonin APC

A daidai lokacin da Jam’iyyar APC ke shirin zabo wanda zai yi mata takarar shugaban kasa a zaben 2023, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya yi…

A daidai lokacin da Jam’iyyar APC ke shirin zabo wanda zai yi mata takarar shugaban kasa a zaben 2023, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya yi wata ganawa da gwamnonin jam’iyyar daga jihohin Arewa.

Da ma dai Shugaba Buhari ya ba da himma wajen ganin an samu sasantawa a tsakanin masu neaman takarar shugaban kasa 23 da ake da su a jam’iyyar.

Wannan shi ne karo na hudu da Buhari ke ganawa da masu ruwa-da-tsaki na jam’iyyar a kasa da mako guda don tabbatar da zaben fidda gwanin jam’iyyar ya gudana cikin nasara.

Mahalarta taron sun hada da Shugaban Kungiyar Gwamnonin , Atiku Bagudu na Jihar Kebbi da Shugaban Kungiyar Gwamnonin Jijohin Arewa, Simon Lalong na Jihar Filato da Nasir El-Rufai na Kaduna.

Sauran su ne, Babagana Zulum na Borno, Abdullahi Sule na Nasarawa, Mohammed Inuwa Yahaya na Gombe, Mai Mala Buni na Yobe, Abubakar Sani Bello na Neja, Abdullahi Ganduje na Kano, Aminu Bello Masari na Katsina, Mohammed Abubakar Badaru na Jigawa sai kuma  Abdurrahman Abdulrazaq na Jihar Kwara.

Sai dai, ya zuwa hada wannan labarin ba a ga shigowar Gwamna Yahaya Bello na Jihar Kogi zauren taron ba.

Kafin tafiyarsa zuwa kasar Spain, Buhari ya gana da gwamnonin APC 22 a ranar Talatar da ta gabata inda ya nuna musu yana da bukatar goyon bayansu wajen zaben wanda zai gaje shi.

Shugaban ya fada wa gwamnoni cewa, dole ne zabin jam’iyyarsu ya zamana “Mutum wanda zai iya bai wa ’yan Najeriya nasara da kwarin gwiwar da suke bukata tun kafin ma zuwan zabubbukan.”