✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

2023: ‘Da biyu jam’iyyu suka tsauwala kudin fom din takara’

Masana sun ce sa gangan jam’iyyu suka tsauwala kudin don din takara

A ’yan kwanakin nan ne dai jam’iyyar APC mai mulki ta sanar da kudin don din takara na zabe mai zuwa ga duk wani mai son tsayawa takara a karkashin jam’iyyar.

Hakan dai ya jawo ce-ce-ku-ce da ma samun mabanbantan ra’ayoyi daga mutane daban-daban.

A jam’iyyar adawa ma ta PDP haka abun yake, inda ita ma ta ninka kudin fama-faman zabe har sau biyu ga masu sha’awar tsayawa takara a cikinta.

Wannan ya sa Aminiya ta tattauna da masana Kimiyyar Siyasa da wasu mambobin jam’iyyun siyayar kasar nan domin jin ra’ayinsu kan tsadar farashin fom din takarar.

A mahangar masana

A wata hira da Aminiya malamin Kimiyyar Siyasa a Jami’ar Bayero da ke Kano, Farfesa Kamilu Sani Fage, ya ce hauhawar farashin ba ya da wata nasaba da karyewar Naira da matsalar tattalin arziki na kasa.

Shehin malamin ya ce da gangan aka yi domin a mayar da siyasa ta masu hannu da shuni, saboda babu wani talaka da zai iya sayen fom.

Ya ce, “Bayan shi kuma ga kudin yakin neman zabe da wasu kudade da za a kashe, zaka ga sun ninka kudin siyen fom din, don haka wannan ba zai bari a yi da talaka ba, ba zai bari a yi da matasa ba, da kuma mata.”

Abun da yake nufi ga dorewar Dimikuradiyya

Farfesa Kamilu Fage ya ce wannan babbar barazana ce a tsarin dimokuradiyya, domin a tsarinta shi ne wadanda mutane suke so su ne ake tsayarwa takara, komai rashin kudinsu.

“Amma yanzu yadda abin ya nuna, mutum ba zai iya fitowa takara ba, idan ba shi da kudi ko kuma bai da ubangida. Saboda mutane masu karsashi ba za su iya fitowa ba sai dai su koma su nemi uban gida, idan kuma suka koma suka samu uban gida to duk cancatarsu, to ba mutane za su yi wa aiki ba , sai dai su yi wa ubannin gidan su.

“Don haka wannan babbar barazana ce a tsarin demokaradiyyar Nijeriya,” inji malamin.

‘Zai iya bude kofar barna’

Bugu da kari, malamin ya ce lamarin zai iya bude kofar barna saboda zai iya sa duk wanda ya sayi fom din tunanin cin riba bayan ya ci zabe.

Ya ce, “Misali, kamar fom na Shugaban Kasa, a tsarin mulki na kasa duka albashinsa na  shekaru hudu ba zai kai miliyan 100 ba.

“Sannan kuma ga kudin da zai kashe na kamfen, wannan zai sa ya yi kokarin mayar da dukiyar kasa tashi, ya rika tsunduma hannu sai yanda ya ga dama zai yi. Zai mayar da siyasa wata hanya ta zuba hannun jari domin cin riba ninkin-ba-ninkin.”

‘Ko nawa ne bai yi tsada ba’

A tattaunawar da Aminiya ta yi da daya daga cikin masu neman tsayawa takara a jam’iyyar APC, Hon. Abubakar Ibrahim, mai neman wakiltar mazabar Kagarko a Majalisar Jihar kaduna, ya ce la’akari da tattalin arziki, fim din ya yi tsada, amma in aka yi la’akari da hidimar da za a yi wa al’umma, ko nawa ne bai yi tsada ba.

Ya ce ba zai ga laifin duk wanda ya dauke sa a haka ba, saboda da yadda kowa yake fahimta da daukar abu.

A cewarsa, jam’iyyarsu ta APC tana yin kokari wajen tafiya da matasa a mulkinta.

“Saboda idan aka duba irin kokarin da shuwagabannin jam’iyyar APC suka yi na sauke farshin fom din tsayawa takara da kashi 40 cikin 100 na kudin ga matasa domin dai kawai su shigo a ci gaba da damawa da su kamar yadda ake yi a yanzu,” inji dam takarar.

Shi kuwa Sani Abdulkadir, mai neman takarar dan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazabar Igabi a jihar Kaduna, cewa ya yi la’akari da farashin da jam’iyyun suka saka, ya nuna karara PDP ta fi son talaka, matasa, da mata.

‘Kora da hali suke wa matasa’

Sani Abdulkadir ya ce a nasa tunanin ana yi wa matasa kora da hali ne duba da yanayin tattalin arziki.

“Idan aka ce matashi ya fito maka da miliyan biyu to bai san inda zai sami kudin ba. Don haka wananan abin ba karamin tashin hankali ba ne ga matasa kuma zai haifar da koma baya a siyarsu,” inji shi.