✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

2023: Dalilan da Atiku ya fi dacewa da takarar shugaban kasa a PDP

Najeriya na bukatar kwararre a kan tattalin arziki ba dan koyo ba.

Zan iya cewa tsohon Mataimakin Shugaban Kasa kuma dan takarar Shugaban Kasar jam’iyyar PDP a zaben 2019, Alhaji Atiku Abubakar, shi ne mutumin ya fi gogewa da sanin halin da siyasar Najeriya take ciki.

Shi ya sa tsunduma bincike don duba wasu batutuwa a kan halin da Najeriya da jam’iyyarmu take ciki a yanzu, a kokarina na tabbabtar da gaskiyar fahimtata.

A matsayina na mai nazari da bibiyar halin da jam’iyyar PDP take ciki, ina iya cewa a halin da take ciki a yanzu tana bukatar kwararre wanda zai hada kan jiga-jiganta ya kare ta daga rushewa ko yagewa.

Kace-nace da mai da martani da rigingimu da suka dabaibaye jami’yyar tun daga shugabancin kasa zuwa na shiyya da jahohi ba bakon abu ba ne.

Hakazalika fadi-tashin da wasu kusoshin jam’iyyar ke yi inda kowannensu ke kokarin ganin ya kafa yaransa a shugabancin jam’iyyar, maimakon kashe wutar rikicin da ke cin ta.

Wani bincike da masana suka yi ya nuna wannan halin da babbar jam’iyyar adawa take ciki ba bakon abu ba ne a siyasa ko rayuwa, inda kowa yake kokarin kare muradinsa.

Shi ya sa masanin siyasa dan kasar Jamus, Ralph Dahrendorf, ya ce rigima domin kare bukata ba laifi ba ne matukar bukatar za ta biya; A karshe dai dole mutum daya ne zai yi nasara.

Ya ce, irin wannan rigima kan yin nasara wajen tabbatuwar cigaba mai dorewa ko samun fahimta tsakanin mutane masu bambancin ra’ayi, ba tare da su din sun hade kansu ba, ba kuma tare da wani alkawari ba, sai dai kawai saboda tsawatarwar da wasu za su yi.

Idan aka lura da yadda aka fara yunkurin tsige shugaban jam’iyyar na kasa, Prince Uche Secondu, wanda kimanin wata uku ya rage masa ya gama wa’adinsa da kuma wasu rigingimu da suka dabaibaye jam’iyyar, har wasu suke sauya sheka zuwa jam’iyya mai mulki, ana iya cewa PDP za ta iya shiga cikin tsaka mai wuya, muddin ba a samu wani kwararre wanda ake girmamawa ba kamar Atiku Abubakar ya shiga tsakani.

Ga wasu dalilan cancantar Atiku:

  1. Kwarewar siyasa da mutunci

Na farko, Atiku shi ne wanda ya fito yana kiraye-kirayen a tabbatar da hadin kai da cewa, “PDP ta fi karfin bukatar wani mutum.

“Ya kamata mu hada kanmu mu sanya jam’iyya a gaba, mu jingine bukatummu, mu bi a hankali kada mu mika kanmu a hannun jam’iyya mai mulki.

“Ba za mu amince ba da tsarin jam’iyya daya ba a Najeriya domin zai hana ’yan Najeriya damar sauya gwamnati a 2023”, kamar yadda ya yi kiran ta hannun kakakinsa, Paul Ibe, a ranar 5 ga Agusta, 2021.

  1. Neman hadin kai

Na biyu, Atiku bai dade ba da yin wani yunkuri na tabbatar da hadin kai tsakaninsa da Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, jigo a PDP wanda suka samu matsala a kan wata bukatarsa a zaben dan takarar shugaban kasar jam’iyyar a 2019.

A yayin zaman da ya gudana a tsakaninsu, Atiku ya ce ’yan Najeriya suna jira ne PDP ta zo ta karbe ragamar mulki daga sama har kasa a 2023.

A matsayinsa na mai fadar gaskiya, marar nuku-nuku, bai boye ba, ya bayyana wa ’yan jarida cewa matsalolin jam’iyya ne suka kai shi Fatakwal domin samun daidaito da Gwamna Wike.

Tabbas ya damu da kawo hadin kai da zaman lafiya a PDP, wadanda ya ce su ne babban tsanin da zai tabbatar da nasarar jam’iyyar a zaben 2023.

  1. Sanin tattalin arziki

Na uku, Atiku yana da kwarewa a kan tattalin arziki da hanyoyin samar da ayyukan yi, musamman a irin wannan lokacin da tattalin arzikin Najeriya yake wani cikin mawuyacin hali a karkashin wannan gwamnati, wadda ta kasa bullo da wasu dabaru da za su bunkasa tattalin arziki.

A 2023 Najeriya tana bukatar kwararre a kan tattalin arziki ba wanda zai kara jefa tattalin arzikinta cikin mugun hali ba.

  1. Damar tsayawa rakara

Yana da kyakkyawar dama duba da yankin da za a tsai da dan takara, idan PDP za ta ba Arewa damar fitar da dan dakara a 2023.

Atiku, wanda ya fito daga Arewa maso Gabas, shi ne wanda mafi karfi da gogewa a jam’iyyar da zai iya karawa da jam’iyya mai mulki ta kowanne fanni, musamman duba da yadda ’yan Najeriya da dama suka yanke kauna daga APC kan rashin cika alkawarin da ta yi musu.

Shi ne wanda ya gana wa Fadar Shugaban Kasa azaba a zaben 2019 da ya gabata.

Yanzu shi ne wanda ya fi kowa cancanta ya dawo da PDP kan mulki 2023 musamman idan shugabannin jam’iyyar sun hadiye maitarsu suka  maida hankalinsu wajen dawowa kan madafun iko a Najeriya.

  1. Samar da ayyuka

Duk da halin da Najeriya take ciki, Atiku yana ci gaba da gudanar da kasuwancinsa cikin kwanciyar hankali.

Wannan ya sa ya mai da hankalinsa kacokam wajen hanyoyin da za a samar da ayyukan yi ga matasa a 2019 yayin kamfen dinsa.

Atiku ya nuna damuwarsa a kan yadda matasa mata da ma maza suke fama da rashin ayyukan yi inda a lokacin 33 zuwa kashi 77 din cikinsu ba su da aiki ko ilimi ko kuma sana’ar hannu.

Ire-iren Atiku ne za su iya magance irin wannan matsala ta hanyar samar wa matasa ayyukan yi da zai rage masu zaman kashe wando da ke kaiwa ga shiga ayyukan ta’addanci wanda talaucine ke haifarwa.

Abun bakin ciki a Najeriya a yau shi ne yadda matasa da ke shiga ayyukan ta’addancin ’yan bindiga da garkuwa da mutane da dangoginsu na tayar da zaune tsaye da kawo matsalar tsaro.

Wannan shi ne babban abun da ya addabe mu saboda yadda gazawar gwamnati wajen samar da ayyukan yi da akalla matasa miliyan uku za su samu da kuma ba wa yan kasuwa damar samar da ayyukan yi a kowacce shekara.

  1. Fahimta da karbuwa a wuri ’yan Najeriya

A ’yan siyasar Najeriya a yanzu, a fahimtata, babu wanda ya san yadda zai hada kan kabilu, addinai da al’adun Najeriya a waje guda kamarsa.

Atiku ya damu da halin da ake ciki, yana da kwarewa da kishin bunkasa tattalin arziki da samar da cigaba.

Tabbas, idan tsohon Mataimakin Shugaban Kasar ya samu dama za ku tabbtar da maganata!

Paschal Oluchukwu, Mai nazari da bibiyar halin da jam’iyyar PDP take ciki.