2023: Dattawan Arewa sun karyata yin ittifaki kan Saraki da Mohammmed | Aminiya

2023: Dattawan Arewa sun karyata yin ittifaki kan Saraki da Mohammmed

    Wakilanmu

Kungiyar Dattawan Arewa (NEF) ta nesanta kanta da rohotannin da suka nuna wai ta amince da tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki da tsohon Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed a matsayin ’yan takarar shugaban kasa na yankin Arewa a karkashin inuwar jam’iyyar PDP.

Sanarwar da shugaban NEF, Farfesa Ango Abdullahi, ya fitar a ranar Juma’a cewa Bala Mohammed da Bukola Saraki ne zabin Arewa a takarar shugaban kasa a PDP ya haifar da ce-ce-ku-ce, musamman a Arewa.

Sanarwar tasa dai ta nuna Saraki da Bala Mohammed da Gwamna Aminu Tambuwal na Jihar Sakkwato da kuma Mohammed Hayatudeen sun hada kai domin cimma yarjejeniya wajen fitar da dan takara a tsakaninsu.

Tuni dai Tambuwal ya barranta daga wannan badakalar tare da cewa shirin da aka yi don cim ma yarjejeniyar ya watse, yayin da tsohon Gwamnan Jigawa Sule Lamido ya ce ba za ta sabu ba.

A nasa bangaren, Daraktan Yada Labarai na NEF, Dokta Hakeem Baba-Ahmed, ya ce yukurin cim ma yarjejeniyar da aka yi wani abu ne da ya shafi ’yan takarar.

A cewarsa, “Gwamna Aminu Tambuwal da takwaransa Bala Mohammed, da tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki da kuma Mohammed Hayatudeen sun tafi sun sanar da tsohon shugaban kasa, Ibrahim Badamasi Babangida aniyarsu tare da neman shawararsa kan batun yarjeniyar tasu.

“A nan ne Babangida ya bukaci Farfesa Ango Abdullahi da ya yi amfani da karfinsa wajen shirya matakan da za su taimaka a cim ma yarjejeniya a tsakanin a ’yan takarar su hudu. Aikin da Farfesa Abdullahi din ya kammala tare da rattaba hannu a kansa.”

Ya kara da cewa, ga baki daya batun bai shafi NEF ba balle kuma a sami hannunta a ciki.

Haka nan ya ce, “Kungiyar Dattawan Arewa ba ta da wata alaka da jam’iyyar siyasa ko dan takara, tana kwatanata adalci wajen ba da damar zaben shugabannin da suka dace a zabubbukan 2023.

“Kungiyar ta gamsu da cewa kowane bangare na kasa ya gudanar da harkokinsa hankali kwance ba tare da wata cutarwa ba.

“Ta kuma yi amannar cewa Arewa na da nagartattun ’yan takarar da ya kamata a bar wakilan jam’iyya da masu kada kuri’a su zabi ra’yinsu.”

Ni na fara tayar da batun yarjejeniyar —Paul Unongo

An ji daya daga cikin dattawan Arewa, Paul Unongo, na kare burin Saraki da Bala Muhammed na neman shugabancin kasa, inda ya fada wa manema labarai a Jos, Jihar Filato cewa, shi ne ya soma fito da batun cim ma yarjejeniya wajen fitar da dan takara a Arewa.

Unongo ya ce, “Kwanaki biyu da suka gabata muka yi taro kan wannan batu a Abuja wanda a karshe muka yarda cewa muddin Arewa ce za ta samar da shugaban kasa a 2023, dole ne dan karar ya fito daga Arewa ta Tsakiya.

“Bayan nazarin ’yan takara hudu da suka nuna kwadayinsu, sai muka ga Gwamna Bala Muhammed da Sanata Bukola Saraki ne suka fi cancanta.”

Kowa na iya shiga zaben fidda gwani —Gwamna Bala

Gwamna Bala Mohammed na Jihar Bauchi ya shaida wa manema labarai a Bauchi cewa, daukar shi a mastsayin daya daga cikin ’yan takarar shugaban kasa daga Arewa karkashin PDP a yarjejeniyar da aka cim ma, hakan ba zai hana sauran ’yan takaran shiga zaben fidda gwani na jam’iyya ba.

Ya kara da cewa, NEF ba ta nuna shi ba sai da ta yi tuntuba da neman shawarwari a wajen masu ruwa da tsaki a sassan kasa kafin ta ce shi da Bukola Saraki sun cancanci zama ’yan takarar shugaban kasa na PDP.

Tare da cewa, duka wadanda ke adawa da yarjejeniyar da aka cim ma suna da damar fadin albarkacin bakinsu.

Da son ranmu muka ziyarci magabata —Saraki

A nasa bangaren, Sanata Bukola Saraki ya ce ra’ayin kai ne martaba yarjejeniyar da Kungiyar Dattawan Arewa ta cim ma.

Saraki ya yi wannan bayanin ne sa’ilin da yake ganawa da wakilan PDP a Minna, babban birnin Jihar Neja.

Ya ce, “A bisa son ranmu muka kusanci magabata don neman tubarraki, ba wai su ne suka bukaci mu sako su ciki ba, ba kuma tilasta mana aka yi don zuwa gabansu ba.

“Muna godiya ga magabatanmu dangane da rawar da suka taka wajen daukar wannan mataki da kuma son ganin hadin kan kasa.

“Yarda da wannan mataki ra’ayi ne, kowa na da damar yin ra’ayinsa,” in ji Saraki.

 

Daga: Bashir Isah, Philip Clement (Abuja), Yusufu A. Idegu (Jos), Ahmed Mohammed (Bauchi) & Abubakar Akote (Minna).