✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘2023: Duk jam’iyyar da ta tsayar da Musulmi 2 takara sai ta riga rana faduwa’

Shi kansa Buhari, dole hakura ya yi da daukar Musulmi a matasyin abokin takara saboda matsalar da hakan zai iya haifarwa

Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir David Lawal, ya ce duk jam’iyyar da ta tsayar Musulmi biyu a matsayin dan takarar shugaban kasar da mataikinsa a zaben 2023 sai ta riga rana faduwa.

Babachir David Lawal ya yi wannan bayani ne a daidai lokacin da ’yan takarar shugaban kasa na manyan jam’iyyun siyasa a Najeriya suke fadi-tashin zabar abokan takararsu.

Ya ce, “Tunanin tsayar da Musulmi biyu, abu ne da ba zai taba samun karbuwa ba a wurin Kiristoci — ni Kirista ne, a cikin Kiristoci nake zama, kuma na san ba za su taba yarda ba.”

A ranar Alhamis Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta ba wa ’yan takarar wa’adin mako guda su mika mata sunayen da abokan takararsu.

Babachir wanda na hannun daman Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar APC ne, ya ce babu yadda za a yi wata jam’iyya ta fitar da dan takarar shugaban kasa da mataimakinsa duk masu bin addini daya kuma ta ci zabe.

Ya bayyana wa shirin siyasa na Politics Today na  tashar talabijin ta Channels cewa hakan ba zai yiwu ba ne saboda bambance-bambancen addini da kabilanci da ke tsakanin ’yan Najeriya suka shiga harkar siyasar kasar.

Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayyar ya ce  jam’iyya tana shiga siyasa ne domin ta ci zabe, kuma idan tana so ta ci zabe, wajibi ne ta duk yi abin da za i sa ta samu kuri’u fiye da abokan hamayyarta.

Abin lura a zaben dan takara

“Jam’iyya na iya samun dan takara mafi nagarta, amma idan ba ta ci zabe ba, bata lokaci ne, babu amfani.

“Don haka, mu sani cewa zabin dan takarar mataimakin shugaban kasa yana da matukar tasiri wajen cin zabe.

“Shi kansa Buhari, a wancan lokacin, dole ya hakura da Tinubu a matsayin abokin tarararsa saboda gudun rudanin da tikitin Musulmi biyu zai iya haifarwa.

“Har yanzu kuma ba mu ga wani abu da ya kawar da wannan tunanin a kasar nan ba, ballantana a iya tsayar da mutum biyu masu addini daya takarar shugaban kasa da mataimakinsa — maimakon haka ma karuwa matsalar yi.”

Ya kuma jaddada bukatar jam’iyyar APC ta yi la’akari da abin da ya dace kafin zaben mataimakin shugaban kasa a zaben 2023.

“Bambance-bambacen addini da kabilanci da bangaranci sun yi yawa a kasar nan, don haka, zai yi kyau idan APC za ta amince da tikitin Musulmi da Kirista saboda mun san abin da PDP za su yi ke nan.”

Shin Babachir zai yi takara

Da aka tambaye shi ko zai so ya zama abokin takarar Tinubu, sai ya ce, “Allah bai yi min ilhamar cewa in yi burin wannan matsayi ba.

“Duk wanda ya kai irin matakin da na kai a addinin Kirista, ya kamata duk abin da zai yi ya nemi zabin Allah Ya ga abin da Allah zai yi.

“Zan yi tunani. Amma a baya ina cikin gwamnati, kuma ban ga wata fa’ida ko amfani da na samu na kashin kai ba.

“Tun da na bar gwamnati na kasance cikin kyakkyawar rayuwa, kuma matsayina na dan kasuwa ni da iyalaina muna cikin farin ciki da jin dadi.