✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

2023: Dukkan kuri’un Arewa maso Yamma na Kwankwaso ne – Buba Galadima

Wani jigo a jam’iyar NNPP, Injiniya Buba Galadima, ya ce dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar, Rabi’u Musa Kwankwaso ne zai lashe dukkan jihohin arewa…

Wani jigo a jam’iyar NNPP, Injiniya Buba Galadima, ya ce dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar, Rabi’u Musa Kwankwaso ne zai lashe dukkan jihohin arewa maso Yammacin Najeriya a zaben 2023.

Galadima ya bayyana hakan ne a tattaunawarsa da gidan talabijin na Arise game da batutuwan da suka shafi harkokin siyasa da zaben 2023.

Ya kuma ce yankin na da masu rajistar zabe miliyan 24, kuma kafatanin kuri’unsu na Kwankwaso ne.

Ya ce, “Kalli Arewa maso Gabashin Najeriya ka gani, ita ma Bauchi ta Kwankwaso ce, haka Gombe da Adamawa da Taraba.

“Inda kawai muke da kalubale shi ne Borno da Yobe saboda APC na da karfi a can.

“Idan ka dauki Arewa ta Tsakiya kuma, ba mu da matsala da jihar Filato, haka Nassarawa, ba kuma mu da haufin komai a Binuwai, Kogi kuwa dama gidansa ce.

“Haka zalika ziyararmu jihar Kwara ta baya-bayan nan mun ga alamun nasara.

“Idan ka koma Kudu ma hakan take, domin jihohin Kuros Riba da Akwa Ibom da Edo da Oyo, duk na mu ne.

“Sai Delta da yanzu muke kokawar samu, da zarar mun same ta 2023 ta mu ce,” inji shi.

Ya kuma ce ko da an murza kambun siyasar kabilanci, ba abin da zai girgiza takarar Kwankwanson, domin suna da yakinin zai yi nasara.