✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

2023: Fastocin Emefiele sun mamaye wajen Babban Taron APC

Tuni dai PDP ta bukace shi ya sauka daga mukaminsa muddin zai tsaya takarar

Fastocin Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele na neman tsayawa takarar Shugaban Kasa a 2023 sun mamaye filin Eagle Square, wajen da jam’iyyar APC ke gudanar da Babban Taronta.

An ga fastocin nasa na da kuma na wasu ’yan takarar irin su Bola Ahmed Tinubu da Gwamnan Jihar Ebonyi, David Umahi da kuma Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi.

Ana dai ganin Emefiele na da sha’awar tsaya wa jam’iyyar APC takarar Shugaban Kasa a 2023.

Kodayake har yanzu bai fito ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar a hukumance ba, amma kungiyoyi daban-daban sun rika kiransa da ya fito takarar.

Ko a ranar Juma’a dai sai da babbar jam’iyyar adawa ta APC ta bukaci ya gaggauta ajiye mukaminsa a matsayin Gwamnan CBN, matukar yana son tsayawa takarar.

Jam’iyyar dai ta ce matakin Gwamnan ya saba da tanade-tanaden Babban Bankin wadanda suka tanadi ma’aikata da shugabanninsa da su nesanta kansu da kowace jam’iyyar siyasa.