✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

2023: Fitar da sakamakon zabe ta na’ura ya zauna daram —INEC

Shugaban INEC ya ce babu batun daina fitar da sakamakon zabe ta na'ura

Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa (INEC ), Farfesa  Mahmood Yakubu ya yi alkawarin cewa hukumar za ta fitar da sakamakon zaben 2013 ta hanyar na’urar zamani.

Mahmood Yakubu ya bayyana haka ne ranar Laraba a Abuja lokacin da ya karbi bakuncin jami’an Rukunin Kamfanonin  Media Trust (masu mallakar jaridun Daily Trust da Aminiya da Trust TV da kuma Trust FM) kan muhawarar zaben da ke tafe.

Shugaban na INEC, ya tabbatar musu cewa a zaben gaba hukumarsa za ta mika sakamakonsa ne ta hanyar na’urar laturoni.

Hakan kuwa na zuwa ne bayan kiraye-kirayen da masu ruwa da tsaki suka cewa, a inganta aikin na’urorin zamani a harkokin zaben kasar domin magance kalubalen da aka samu a zabukan da suka gabata.

Dangane da haka ne Majalisar Dokokin Kasar ta yi wa dokar zaben kwaskwarima. 

A ranar 25 ga watan Fabrairu ne Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari ya sanya hannu kan dokar zabe ta 2022 bayan majalisar ta amince da ita.

Daya daga cikin muhimman abubuwan da dokar ta tanadar akwai shigar da fasaha a harkar zabe.

Sashi na 52(2) na dokar ya ce: “A karkashin sashe na 63 na wannan kudiri, kada kuri’a a zaben da kuma mika sakamako a karkashin wannan kudirin ya kasance daidai da tsarin da Hukumar INEC ta tsara, wanda zai iya hada da yin zabe ta hanyar laturoni.”