2023: Ganduje zai sayi fom din takarar Sanata a Kano | Aminiya

2023: Ganduje zai sayi fom din takarar Sanata a Kano

Abdullahi Ganduje, Gwamnan Jihar Kano
Abdullahi Ganduje, Gwamnan Jihar Kano
    Clement A. Oloyede da Sani Ibrahim Paki

Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje zai sayi fom din neman tsayawa takarar Sanata mai wakiltar Kano ta Arewa a karkashin jam’iyyar APC.

Wata majiya ta ce magoya bayan Gwamnan ne ake sa ran za su saya masa fom din ranar Litinin.

Hakan dai, a cewar wata majiya ya biyo bayan taron da aka yi ne tare da wasu masu ruwa da tsakin jam’iyyar a Fadar Gwamnatin Jihar da ke Kano ranar Lahadi.

Kazalika, yayin taron kuma, an cim ma matsayar amincewa da Mataimakin Ganduje, Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin wanda zai gaji Gwamnan, yayin da tsohon Kwamishinan Kananan Hukumomin Jihar, Murtala Sule Garo zai kasance mataimakin dan takarar.

Yanzu haka dai Sanata Barau Jibrin ne ke wakiltar mazabar a Majalisar Dattijai.

Sai dai tun bara yake takun-saka da Gandujen shi da wasu ’yan majalisa da ke wa kansu lakabi da G-7, karkashin Sanatan Kano ta Tsakiya kuma tsohon Gwamnan Jihar, Ibrahim Shekarau bisa rikicin shugabancin APC a Jihar.

Sai dai a ranar Juma’a Kotun Koli ta kawo karshen takaddamar, inda ta tabbatar da shugabancin tsagin Gwamna Ganduje, karkashin Abdullahi Abbas.

Sanata Barau dai wanda tuni ya bayyana aniyar shi ta neman takarar Gwamnan Jihar ya ce zai ci gaba da zama a jam’iyyar ta APC.