✕ CLOSE Kiwon LafiyaRa’ayoyiRa'ayin AminiyaRahotoAminiyar KurmiHotunaGirke-GirkeSana'o'iKimiyya da Kere-Kere

2023: Gwamna Buni ya gabatar da kasafin N163.2bn

Buni ya ce kasafin na 2023 ya dara na 2022 da kashi 0.49 cikin 100.

Gwamna Mai Mala Buni na Jihar Yobe, ya gabatar wa Majalisar Dokokin jihar daftarin Naira biliyan 163.2 a matsayin kasafin kudin jihar na badi.

Da alama kasafin wanda Gwamnan ya gabatar a ranar Alhamis, zai maida hankali kan ci gaba da ayyukan da aka assasa da inganta tattalin arzikin jihar.

Da yake jawabi yayin gabatar da kasafin, Buni ya ce kasafin na 2023 ya dara na 2022 da kashi 0.49 cikin 100.

Ya kara da cewa, an ware biliyan N87.8 domin manyan ayyuka, sannan naira biliyan 75.4 don ayyukan yau da kullum, wanda hakan ya yi daidai da kashi 57 da 43 na jimillar kasafin.

A nasa bangaren, Shugaban Majalisar jihar, Alhaji Ahmed Mirwa ya yaba wa Gwamna Buni bisa kokarin da ya yi wajen aiwatar da wasu manyan ayyukan ci gaba a jihar.

Mirwa ya kuma ba da tabbacin cewa Majalisar ba za ta bata lokaci ba wajen yin bita da kuma amincewa da kasafin na 2023.

(NAN)