✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

2023: Gwamnan Jigawa ya sayi fom din takarar Shugaban Kasa a APC

Tuni dai Gwamnan ya garzaya Abuja don neman tabarrakin Buhari

Gwamnan Jihar Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar ya bi sahun masu zawarcin takarar Shugaban Kasa a karkashin jam’iyyar APC a zaben 2023 mai zuwa.

Gwamnan dai ya sayi fom din takarar ne a hedkwatar jam’iyyar ta kasa da ke Abuja a ranar Laraba.

Badaru dai da farko yana kokarin fitowa takarar Sanata ne a zaben mai zuwa, kafin daga bisani ya canza shawararsa zuwa takarar Shugaban Kasa bayan wani taro da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a fadar gwamnatin Jihar ranar Talata.

Ko da yake har yanzu dai ba a san makasudin canza shawarar tasa ba, amma an ce ya shaida wa mahalarta taron cewa ya fuskanci matsin lamba ne daga abokan shi kan ya fito takarar.

Wata majiya ta shaida mana cewa tuni Gwamnan ya nufi Abuja don neman tabarrakin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari gabanin sayen fom din takarar.

Aminiya ta gano cewa matakin da Kungiyar Gwamnonin APC ta dauka na neman Badarun ya fito takarar, kuma hakan bai rasa nasaba da yunkurin tunkarar ko-ta-kwana, idan ma jam’iyyar ta yanke shawarar ba da takara a Arewa.

Hadimin Gwamna Badarun kan harkokin yada labarai, Habibu Nuhu Kila, ya tabbatar da gaskiyar labarin.

Ya ce, “Gaskiya ne Gwamna Badaru ya tafi Abuja domin sayen fom din saboda ya cancanta.

“Zai dora a kan kyawawan manufofin Shugaba Buhari in ya ci zabe,” inji Habibu Kila.