Daily Trust Aminiya - 2023: Hakikanin dambarwar da ke faruwa a Fadar Shugaban Kasa
Subscribe

2023: Hakikanin dambarwar da ke faruwa a Fadar Shugaban Kasa

A kwanakin baya ne Fadar Shugaban Kasa ta sanar da kwace madafun ikon wasu ma’aikatun da suke karkashin Mataimakin Shugaban Kasa Farfesa Yemi Osinbajo, inda daga wannan lokacin aka bukaci ya rika sanar da Shugaban Kasa kafin ya dauki duk wani mataki.

Ma’aikatun da suke karkashin Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osibanjo sun hada da Hukumar NEMA da Hukumar Kula da Iyayokin Kasa da Hukumar Bunkasa Al’ummun Da ke Kan Iyakokin Kasa da Cibiyar Horar da Manyan Ma’aikata (NIPSS). Haka kuma shi yake Shugabantar Kwamitin Gudanarwa na Kamfanin Wutar Lantarki na Neja-Delta (NDPHC) da kuma Hukumar Sayar da Hannun Jari (NPC).

Kafin nan, an fara ne da canja Kwamitin Tattalin Arziki da ke karkashin Osibanjo, inda aka maye gurbinsa da Kwamitin Bayar da Shawara kan Tattalin Arziki (EAC), kuma aka bukaci sabon kwamitin ya rika kai rahoto kai-tsaye ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari; wanda hakan ke nufin cire tattalin arzikin kasar daga karkashin kulawar Osinbajo.

Duk da cewa babu wani dalilin da Gwamnatin Tarayya ta bayar kan wannan sabon sauyi amma a wata sanarwa da Ofishin Mataimakin Shugaban Kasa ya fitar, an bayyana cewa Mataimakin Shugaban Kasar ba ya karya doka wajen gudanar da ayyukansa, musamman wajen tafiyar da ma’aikatu ko hukumomin da yake kula da su.

Kuma duk kokarin da ake yi don yayyafa wa wutar ruwa, lamarin yana ta kara tayar da kura, inda wadansu suke tunanin akwai wadanda suke kokarin ganin bayan Mataimakin Shugaban Kasar.

Wata majiya da Aminiya ta tuntuba kan lamarin a Ofishin Shugaban Kasa ta ce sabon canjin bai rasa nasaba da shirye-shiryen zaben shekarar 2023 bayan Shugaba Buhari.

Wata majiyar kuma ta ce duk da cewa Kwamitin Tattalin Arzikin bai tsinana komai ba, amma canja kwamitin da cire shi daga karkashin kulawarsa ba saboda rashin aiki ba ne. “Ba wai an cire Kwamitin Tattalin Arziki a karkashin kulawar Osinbajo ba ne saboda rashin kokari ko kuma saboda ba ya aikinsa, duk da cewa bai yi wani aikin a zo a gani ba. Wannan sabon sauyin ana yi ne saboda shirye-shiryen zaben 2023,” kamar yadda majiyar ta bayyana.

Shi ma wani Sanata wanda ba ya so a ambaci sunansa da Aminiya ta tuntuba kan lamarin, cewa ya yi dole akwai batun mulki da siyasa a ciki, inda ya yi zargin cewa ana kokari ne a ga yadda za a yi watsi da yankin Kudu maso Yamma a zaben 2023.

“Duk wadannan sauye-sauyen ana yi ne saboda lissafin zaben 2023. Amma ni a tunanina, fada da yankin Kudu maso Yamma ba zai haifar wa siyasar kasar nan da mai ido ba,”inji shi.

Da yake karin bayani kan yadda yankin Kudu maso Yamma ya tallafa wa Shugaban Kasa Muhammdu Buhari wajen lashe zabe tun daga na shekarar 2015, ya ce kamata ya yi su ma ’yan Arewa su rama wa kura aniyarta.

Wani babban dan siyasa daga Arewa ya alakanta sabon sauyin da siyasar shekarar 2023. Da yake bayani kan lamarin, dan siyasar ya ce akwai abubuwa da suke gudana a tsakanin na kusa da Shugaban Kasa a yanzu haka game da shirye-shiryen zaben shekarar 2023. “Kowa yana son ya zama shi ne kan gaba wajen kokarin maye gurbin Shugaban Kasar bayan ya kammala wa’adinsa a zaben 2023.

“Babban abin da suke so su yi shi ne, musamman a wannan lokaci da Shugaban Kasa yake shan wahalar mulki, a kawar da hankalin mutane musamman ta hanyar sanya rade-radi da jita-jita a tsakanin mutane game da Mataimakin Shugaba Kasa.

“Amma dai babu laifi ’yan Najeriya su yi irin wadannan rade-radi ko tunanin cewa sabon sauyin yana da alaka da rikicin da ke tsakanin Gwamna El-Rufa’i da Asiwaju Tinubu da Osinbajo shi kansa.

“Ba zai yiwu ka cire irin wadannan abubuwan a siyasa ba, domin yana cikin ayyukan siyasa da gwamnati. Amma dai ina fata Fadar Shugaban Kasa za ta fayyace asalin abin da ke wakana cikin sauri domin magance rade-radi masu rikitarwa. Lallai ana bukatar haka,” inji shi.

Idan ba a manta ba, a watan Yuli Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce ba zai zabi wanda zai gaje shi ba, inda ya ce, “Maganar wanda zai gaje ni, ina ganin wannan abin dariya ne domin idan har na zabi wani, to zan jefa shi cikin matsala ce kawai. Kawai duk wanda yake son zama Shugaban Kasa ya dage kamar yadda na yi. Amma ya kamata wadanda suke neman kujerar su tuna cewa ni ma na nema sau uku, kafin Allah Ya ba ni nasara. Ina godiya ga Allah da fasahar zamani da katin zabe na dindindin.”

Akwai matsala – Kungiyar Afenifere

Da take jawabi game sauyin da aka samu, Kungiyar Yarabawa ta Afenifere ta ce bisa lura da abin da ke gudana akwai yuwuwar ana kokarin mayar da Mataimakin Shugaban Kasar saniyar ware ne.

Kakakin Kungiyar, Yinka Odumakin a wata zantawa da wata jarida, ya  ce duk da cewa ba za su yi gaggawar yanke hukunci ba, amma sun san cewa akwai matsala a kasa.

“Muna nan muna kallon abin da ke wakana, kuma muna lura da komai cikin natsuwa, muna jira ta yi wari domin mu ji. Amma dai ba za mu yanke hukunci ba.

“Ba ma so mu yi gaggawar yanke hukuncin cewa a kan zaben 2023, domin muna bukatar karin bayani don sanin hakikanin abin da ya faru, ko dai game da zaben 2023, ko rashin bin ka’ida. Amma abin da ya faru ya nuna cewa akwai matsala. Amma ba ma so mu fito fili mu bayyana abin da ke faruwa, kada a ce muna nuna cewa an yi wa Bayarabe ba daidai ba.

“Da sannu za mu sanar da matsayarmu, amma lura da abin da yake wakana, a fili yake cewa an mayar da Ofishin Mataimakin Shugaban Kasan mara amfani.”

Fulani ne ke neman ci gaba da mulki – Kungiyar Ohanaeze

Da take mayar da martani, Kungiyar Ohanaeze ta kabilar Ibo ta zargi sauye-sauyen da ke gudana da cewa Fulani ne suka kokarin ci gaba da mulki har bayan shekarar 2023, kuma ba su yi mamakin haka ba.

Kakakin Kungiyar, Uche Achi-Okpaga ne ya bayyana haka a wata zantawa da wata jarida (ba Aminiya ba), inda ya ce, “Idan har za su iya cire Babban Jojin Najeriya daga kujerarsa, to mene ne ba za su iya yi ba? Kana tunanin ba za su iya yi wa Mataimakin Shugaban Kasa ba? Za su iya yin komai. Yanzu ba a yin amfani da ka’idar mulki. Akwai Fulanin da suke so su ci gaba da mulki har bayan shekarar 2023 ce.”

Idan lokaci ya yi za mu yi magana – PDP

A jawabin, Jami’iyyar PDP ta ce yanzu ba maganar bangaren da za a ba takara ba ce a gabansu, domin “yanzu haka muna kotu ne muna so mu kwace hakkinmu na zaben da ya gabata. Don haka ba za mu yi magana ba a game da zaben 2023 yanzu. Babu wanda ya san abin da zai faru gobe, amma muna maganar shekarar 2023,” kamar yadda Shugaban PDP na kasa Uche Secondus ya bayyana.

Maganar mulki ne a gabanmu ba zaben 2023 ba – APC

Ita ma Jam’iyyar APC cewa ta yi ba ta da lokacin yin maganar zaben shekarar 2023 a yanzu, domin harkokin mulki ne a gabansu.

Kakakin Jam’iyyar, Lanre Issa-Onlu ne ya bayyana haka, inda ya ce, “Maganar gaskiya ita ce yanzu mu maganar mulki ne a gabanmu. Mun yi wa ’ya’yan jam’iyyarmu gargadin cewa ba ruwansu da maganar zaben mai zuwa ko kuma tunanin yankin da za a ba takara.”

More Stories