✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

2023: Hare-hare kan ofisoshinmu ba za su hana mu gudanar da zabe ba – INEC

Yakubu ya ba da tabbacin hukumar za ta sake mallakar kayayyakin da asarar ta shafa kafin zaben.

Hukumar Zabe Ta Kasa (INEC) ta ce hare-haren da ake kai wa ofisoshinta da ma ma’aikatanta ba za su hana ta gudanar da babban zaben 2023 cikin nasara ba.

Shugaban hukumar, Farfesa Mahmoud Yakubu ne ya bayyana haka a lokacin da ya karbi bakuncin tawagar Kungiyar Hadin Kan Kasashen Afirka (AU), karkashin jagorancin Phumzile Mlambo-Ngcuka, ranar Litinin a Abuja.

Yakubu ya ce tuni an yi asarar wasu kayan aikin da aka tanada don zaben na 2023 sakamakon hare-haren da aka kai ofishin INEC a wurare daban-daban a fadin kasar.

Ya ba da tabbacin hukumar za ta sake mallakar kayayyakin da asarar ta shafa kafin zaben.

Ya kara da cewa, duk da nasarorin da INEC ke samu wajen shirye-shiryenta, fannin tsaron kasar abin damuwa ne, musamman hare-haren da ake kai wa ofisoshin hukumar.

Ya ce a cikin mako ukun da suka gabata, an kai wa ofishinsu hari a wasu Kananan Hukumomi uku a jihohi daban-daban.

Tun farko da yake jawabi, shugaban tawagar Mlambo- Ngcuka, ya ce sun zo Najeriya ne domin nuna goyon baya ga kasar dangane da zaben da za ta gudanar a 2023.