2023: Ina da gogewar da zan iya ceto Najeriya —Saraki | Aminiya

2023: Ina da gogewar da zan iya ceto Najeriya —Saraki

Bukola Saraki
Bukola Saraki
    Abubakar Muhammad Usman

Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Bukola Saraki, ya bayyana kansa a matsayin wanda yake gogewar da zai iya ceto Najeriya daga halin da take fuskanta idan har aka zabe shi shugaban kasa a 2023.

Saraki, wanda ke neman takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, ya bayyana haka ne yayin wata ziyarar da ya kai birnin Akure, Jihar Ondo don neman goyon baya daga wakilan jam’iyyar jihar.

Ya ce zaben 2023 zai kawo sauyi ga Najeriya, inda ya ce kasar tana bukatar shugaban kasa wanda ya fahimci tattalin arziki, kana zai iya sadaukarwa wajen ceto ta daga kalubalen da take fuskanta.

Saraki ya ce Najeriya na bukatar shugaban kasa mai kuzari wanda zai iya tafiyar da ita na tsawon sa’a 24 ko sama da haka idan abubuwa suka cakude.

A cewarsa, gogewarsa a harkar siyasa da kuma abubuwan da suka faru a baya sun nuna cewa yana da nagartar zama shugaban kasa.

Ya kuma kara da cewa ya kawo sauyi da ci gaba mai tarin yawa a Jihar Kwara lokacin da ya yi gwamnan jihar.

Saraki ya yi alkawarin cewa zai maimaita irin nasarorin da ya samu a lokacin da yake Shugaban Majalisar Dattawa idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa a 2023.

Da yake jawabi a wajen taron, Shugaban Jam’iyyar PDP na Jihar Ondo, Mista Fatai Adams, ya bayyana cewa lokacin da Saraki yake rike da mukaminsa ya juya akalar majalisar dokokin Najeriya yadda ya kamata.

Ya bayyana shi a matsayin dan jihar saboda matarsa ​​da mahaifiyarsa jihar ce.

Har wa yau, Mista Earl Osaro, Darakta Janar na Kungiyar Yakin Neman Zaben Saraki, ya bukaci wakilan jam’iyyar na jihar da su mara mishi baya.

Kazalika, ya ce Saraki wata gada ce tsakanin Arewa da Kudu, Musulmi da Kirista wanda zai iya ceto Najeriya daga kalubalen da take fuskanta.