✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

2023: INEC ta karbi kashin karshe na na’urorin BVAS

Wannan shi kashin karshe na BVAS da INEC ta karba.

Yayin da ya rage kasa da mako takwas kafin zaben 2023, Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), ta tabbatar da karbar kashin karshe na na’urorin tantance masu kada kuri’a (BVAS) a ranar Talata.

Babban Kwamishina kuma Shugaban Kwamitin Ilmantar da Masu Zabe na hukumar, Festus Okoye ne ya tabbatar da hakan ranar Laraba a Abuja.

“Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu tare da manyan jami’an hukumar sun kasance a Babban Filin Jirgin Sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja don karbar BVAS.

“Jami’an Kwastam da na tsaro ne suka tarbi tawagar INEC a filin jirgin.

“Kuma domin tabbatar da an karbi na’urorin cikin sauki ya sa aka rarraba inda aka sauke su da suka hada da Abuja da Kano da Legas da kuma Fatakwal,” in ji Okoye.

Ya kara da cewa, sama da wata hudu jiragen sama suka yi ta isar da BVAS a wasu filayen jirgin sama don tura su zuwa jihohin kasar.

Ya ce kawo yanzu INEC ta kammala karbar adadin na’urorin BVAS da take bukata don gudanar da zaben na bana.

Aminiya ta ruwaito cewa, na’urar BVAS da ta tattara sakamakon zabe (IReV), na’urori ne wadanda INEC ta shirya yin amfani da su a zabe mai zuwa don gudanar da sahihin zabe.

Okoye ya yaba wa daukacin ‘yan kasa bisa goyon bayan da suke nuna wa hukumar don tabbatar da ta shirya zabe mai tsafta.