✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

2023: Jonathan na nan daram a PDP – Saraki

Saraki ya kuma ce babu kamshin gaskiya ko kadan a jita-jitar da ake yadawa cewa Jonathan zai koma APC.

Tsohon Shugaban Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Bukola Saraki ya ce tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan a shirye yake da ya bayar da kowacce irin gudunmawa wajen ganin jam’iyyar PDP ta sake dawowa kan karagar mulki a 2023.

Ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawarsa da ’yan jarida, jim kadan bayan jagorantar Kwamitin Sasanta ’Ya’yan Jam’iyyar na Kasa domin wata tattaunawa a gidan tsohon Shugaban dake Abuja ranar Talata.

Saraki ya kuma ce babu kamshin gaskiya ko kadan a jita-jitar da ake yadawa cewa Jonathan zai koma jam’iyyar APC mai mulki.

Wasu masu ruwa da tsaki a jam’iyyar dai sun jima suna hankoron ganin tsohon Shugaban ya sake tsayawa takarar Shugaban Kasa a 2023.

Saraki ya ce, “Mun tattauna a kan irin rawar da ya kamata tsohon Shugaban Kasa kamarsa ya taka, kuma mun fito cike da kwarin gwiwar cewa zai taimakawa PDP ta kai ga gaci.

“Mun fara da Jonathan ne a matsayinmu na kwamitin da aka kafa domin sasanta ’ya’yan jam’iyya da nufin dinke dukkan barakar dake cikinta.

“Gaskiya wannan tattaunawa ce mai matukar fa’ida.

“Ya ba mu shawarwari, ya fada mana ra’ayinsa, kuma mun ji dadi sosai.

“Ya tabbatar mana cewa yana nan daram a jam’iyyarmu, kuma a shirye yake ya bayar da kowacce irin gudunmawa wajen sake dawo da martabarta,” inji Saraki.

Saraki ya ce tattautanawar wacce aka shafe kusan sa’o’i biyu ana yi ta sami halartar tsoffin Gwamnonin jihohin Katsina da Gombe da Kuros Ribas da Imo, da tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya Anyim Pius Anyim da tsohuwar Shugabar Masu Rinjaye a Majalisar Wakilai, Mulikat Adeola-Akande.

An dai kaddamar da kwamitin na Saraki ne watanni kadan bayan PDP ta fadi a zaben Shugaban Kasa na 2019 da nufin gyara kura-kuran da suka kai ga rashin nasarar domin ta karbe mulki daga APC a 2023.