✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

2023: Kayode Fayemi ya fito takarar shugaban kasa

Shugaban Kungiyar Gwamonin Najeriya zai fito ya yi alkawarin kawo hadin kai na shugabanci nagari.

Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya kuma Gwamnan Jihar Ekiti, Kayode Fayemi, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2023.

Mista Fayemi zai fito takarar shugaban kasa ne karkashin inuwar a Jam’iyyar APC, mai mulki, wadda za ta gudanar da zaben fitar da dan takarar shugaban kasarta a ranakun 30 da 31 ga watan Mayu da kuma 1 ga watan Yuni, 2022.

Da yake sanar da aniyar tasa a Abuja ranar Laraba, Fayemi ya yi alkawarin kawo shugabanci nagari da kma tabbatar da hadin kai idan aka zabe shi shugaban kasa a babban zaben na 2023.

A halin yanzu, Fayemi ya shiga jerin masu zawarcin kujerar shugaban kasa a jam’iyyar APC da suka hada da Mataimkain Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo; da Uban Jam’iyyar ta Kasa, Bola Tinubu da kuma Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi.

Sauran sun hada da Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello; Gwamnan Ebonyi, Dave Umahi; da tsohon Gwamnan Jihar Imo, Santa Rochas Okorocha.

Akwai kuma Ministan Kwadago da Ingantuwar Aiki, Sanata Chris Ngige; da Gwamnan Jihar Kuros Riba, Ben Ayade da dai sauransu.