✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

2023: Limami zai tsaya takarar Gwamna a Adamawa

Malamin dai tsohon ma’aikacin Rediyo Gotel ne da ke Yola kuma mai fatawar addinin Musulunci.

Babban Limamin Masallacin Gidan Talabijin na Jihar Adamawa (ATV), Malam Abdulkadir Isa ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar Gwamnan Jihar.

Malamin dai tsohon ma’aikacin Rediyo Gotel ne da ke Yola, sannan mai fatawar addinin Musulunci.

Ya bayyana hakan ne yayin zantawarsa da ’yan jarida a ranar Laraba a Yola.

Malam Abdulkadir ya ce babu ko tantama a batun tsayawarsa takarar, shi ya sa ya bayyana kudirinsa na tsayawa takarar.

A cewarsa, “Kasancewar kowa na da irin tasa fasahar da kuma hangen nesa da karfin zuciya da dogorona ga Allah bisa duk wata kaddara da za ta sameni ya sanya na yanke shawarar tsayawa takarar Gwamna a jihar.”

Daga nan sai ya bukaci  jama’a da su sanya shi a addu’a, yana mai cewa manufarsa za ta farantawa al’ummar jihar rai ba tare da nuna kowane irin bambancin addini ba domin kawo canjin da jihar ke bukata.

Limamin ya ce manufar fitowarsa ita ce kokarin ceto jihar daga halin da take ciki.

Ya ce, “Na zaga wasu kasashe a duniya na ga yadda talaka yake da daraja. Kuma ni na dauki takarar nan a matsayin ibada zan yi, ma’ana abin da Allah zai yi sakayya da shi.

“Na sani ba dukkan limami ne ko almajirin ilmi zai iya yunkurin fitowa ba a irin wannan fagen don tsoron maganganun masu magana.” inji shi.

Ya kuma yi kira ga al’ummar jihar da su goya masa baya domin ya kai ga gaci.