✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

2023: Manyan abubuwa 7 da za su iya tarwatsa APC a Kano

Matsalolin ba wai Kano suka shafa ba har da uwar jam’iyyar a matakin kasa.

Wasu abubuwa da suka taso a cikin Jam’iyyar APC mai mulkin Jihar Kano, jihar da take da tasiri a siyasar kasar nan saboda yawan jama’ar da take da su, wadanda wasu daga cikin matsaloli ba wai Kano suka shafa ba har da uwar jam’iyyar a matakin kasa.

Babban lamarin dai ya taso ne a lokacin da Jam’iyyar APC ta bayar da sanarwar dakatar da dan Majalisar Wakilai mai wakiltar Karamar Hukumar Birni da Kewaye, Sha’aban Sharada na tsawon wata 12.

Sha’aban da Ganduje

An dauki tsawon lokaci ana sa zare a tsakanin Gwamana Abdullahi Ganduje da Sha’ban Sharada wanda shi ne tsohon mai taimaka wa Shugaban Kasa a kan kafafen sadarwar zamani.

A cikin takardar dakatar da dan majalisar, Shugaban Jam’iyyar a Karamar Hukumar Birni da Kewaye, ya ce an dakatar da dan majalisar ne, bisa laifin yin wasu abubuwa na cin dunduniyar jam’iyyar da kuma cin zarafin Gwamnan Jihar.

A watan Fabrairun da ya gabata Sharada ya zargi Gwamna Ganduje da shugabannin Jamiyyar APC na jihar bisa hana shi hakkinsa na sabunta rajistarsa a mazabarsa, zargin da Gwamnan ya musanta.

A makon jiya ne aka samu rahoton cewa matasa sun cika sakatariyar Jam’iyyar APC ta Kasa suna zanga-zanga cewa Gwamna ganduje yana kokarin tarwatsa jam’iyyar a Jihar Kano.

Matasan da ake dauka magoya bayan tsohon na hannun damar Shugaban Kasa ne.

Mutane da dama suna ganin cewa Sha’aban ba ya da matsala da Gwamna Ganduje a kan kansa sai dai da mutanen da ke kewaye da Gwamnan wadanda kuma ’yan asalin Karamar Hukumar Birni da Kewaye ne wadanda suka hada da Kwamishinan Ayyuka na Musamamn Alhaji Mukhtari Is’hak Yakasai da Kwamishinan Watsa Labarai Kwamared Muhammad Garba.

Yakasai ya tsaya a zaben fidda-gwani tare da Sha’aban a kujerar dan Majalisar Wakilai inda ake kyautata zaton shi ya lashe zaben, amma daga baya aka ba Sharada tikitin takarar inda ake zargin an yi haka ne daga Abuja. Haka an sake kwatawa a daidai lokacin zaben kananan hukumomi, inda dan takarar da Kwamared Garba yake mara wa baya ne ya samu nasara a kan dan takarar Sha’aban.

Masu sharhi a kan al’amuran yau da kullum suna ganin cewa ba batun dakatarwar da aka yi wa Sha’aban ne lamarin da ke neman tarwatsa jam’iyyar ba, akwai abubuwa da dama da suka dade suna damun jam’iyyar a jihar.

Rigimar shugabancin jam’iyya

Daga cikin abubuwan akwai batun yakin da ake yi wajen neman kujerar shugabancin jam’iyyar ta APC a tsakanin Shugaban Riko na jam’iyyar, Alhaji Abdullahi Abbas da tsohon shugaban rusasshiyar Jam’iyyar CPC Alhaji Adamu Haruna Zago.

An hakikance mutanen biyu dukkansu na kusa da Gwamna Ganduje ne, sai dai abu ne mai matukar wahala a gan su a tare a duk wasu tarurruka saboda adawar da ke tsakaninsu.

Tsakanin Barau da Garo da Gawuna

Wani lamarin shi ne rigimar da ke tsakanin Sanata Barau Jibrin na Kano ta Arewa da Kwamishinan Kananan Hukumomi Murtala Sule Garo.

Lura da cewa dukkansu sun fito daga yanki daya, burin da kowa ke da shi da kuma karfin son juya sitiyarin jam’iyya shi ne abin da ke neman tarwatsa su wanda ya janyo yaransu ’yan jagaliya ke tayar da fitina a duk lokacin da wani taro ya hada su.

Yayin da Barau ke shaukin haye kujerar Gwamna a bayan Ganduje, a gefe guda Garo zai tsaya ne a matsayin Mataimakin Gwamna a takarar da ake jin Mataimakin Gwamna Ganduje, Alhaji Nasiru Yusuf Gawuna yake nema.

Shekarau da Ganduje

Duk da cewa Gawuna ya yi aiki a karkashin gwamnoni uku tun daga lokacin da aka fara mulkin dimokuradiyya a 1999, inda ya rike Shugaban Karamar Hukumar Nasarawa har karo biyu, ya fara siyasa ne a karkashin Sanata Malam Ibrahim Shekarau (Kano ta Tsakiya) lokacin yana Gwamnan.

Ana ganin a yanzu Shekarau ya nesanta kansa da gidan gwamnatin.

Majiyarmu daga gidan siyasar Shekarau ta tabbatar mana da cewa abubuwa ba sa tafiya daidai a tsakanin shugabannin jam’iyyar a jihar da Sanata Ibrahim Shekarau lamarin da majiyar take gani a matsayin rashin kyautatawar da ake zargin Gwamna Ganduje ya yi wa ubangidansu bayan sun yi masa kokarin da ya dawo kan kujerar mulki a shekarar 2019.

APC da mutanen Buhari

Wata kungiya mai goyon bayan Buhari a karkashin jagorancin Alhaji Shehu Dalhatu ta rubuta takardar korafi ga kwamitin da ke kula da aikin rajistar ’ya’yan Jam’iyyar APC cewa akwai rashin adalci game da yadda aikin sabunta rajistar da ake yi a Jihar Kano ke tafiya inda ta ce ana nuna wariya ga ’ya’yan jam’iyyyun da suka kulla majar da ta haifar da APC.

Sai dai a cikin takardar martani da manyan kusoshin waccan tafiya ta tsofaffin jam’iyyun hada-ka suka sanya wa hannu sun ce masu waccan da’awa suna yi ne kawai don hada kai da ’yan adawa wajen ganin aikin na sabunta rajista bai samu nasara ba.

Wadanda suka sanya hannu a kan waccan takardar martanin sun hada da Sakataren Gwamnatin Jihar Kano Alhaji Usman Alhaji (Jami’yyar CPC) da Sanata Kabiru Gaya da Sanata Barau Jibrin (Jam’iyyar ANPP).

Jamiyyar APC Akida ta Kwamanda

Kwanan nan dan ga-nikashe-nin Shugaban Kasa Abdulmajid Danbilki Kwamanda ya kafa wata jam’iyya mai suna APC Akida lamarin da ya janyo aka kore shi daga Jam’iyyar APC.

Shi ma Kwamandan dan asalin Karamar Hukumar Birni da Kewaye ne.

Shigowar jiga-jigan ‘yan siyasa cikin APC

A daidai lokacin da aka gudanar da taron Ranar Dimokuradiyya a jihar, Jamiyyar APC ta karbi wadansu jiga-jigan ’yan siyasa wadanda suka yi takarar Gwamna a jam’iyyun daban-daban.

Ana ganin wannan lamarin zai kara kawo tabarbarewar jam’iyyar musamman abin da ya shafi takarar kujerar Gwamna. Baya ga kusoshi uku da suka hada da Salihu Sagir Takai da A.A. Zaura da kuma Umar Yakubu Danhassan wadanda ake tunanin za su nemi su gaji kujerar Gwamna Ganduje, akwai kuma mutane irin su Mataimakin Gwamna Dokta Nasiru Gawuna da Sanata Barau wadanda ake gani za su iya gadar kujerar.

Haka kuma akwai Barista Muhyi Magaji Rimin Gado da wani babban ma’aikaci a Kamfanin NNPC wato Alhaji Inuwa Waya duk suna cikin wadanda za su nemi takarar Gwamnan Kano kamar yadda bayanai suka nuna.

Gwamna Ganduje ya yi amfani da hikima kan yadda zaben wanda zai tsaya takarar Gwamna zai kasance inda ya ce “Wakilan jam’iyya ne za su yi wannan aiki.

Ba abu ne mai sauki ga Gwamna ya yi wannan aiki ba saboda lamari irin na siyasa. Lokaci ne kawai zai bayyana hakan. Sai dai kuma abu ne da za a iya warware shi a siyasance.”

Yayin da aka tambaye shi game da halayen wanda zai gaje shi sai Gwamnan ya ce, “Idan na gaya maka wadannan halaye to kai ma da kanka za ka fara hada su da ’yan takarar daga nan za ka ce ai ga wanda aka tsayar.

Wannan aikin wakilan jam’iyya ne” Haka jawabin Gwamna Ganduje na kwanan nan cewa zai ci gaba da siyasa bayan ya sauka daga Gwamna abu ne da yake nuni da cewa jam’iyyar tana tsaka-mai-wuya.

Yayin da mutane da dama ke tunanin Gwamnan na son yin takarar Mataimakin Shugaban Kasa ne tare da Cif Bola Tinubu wanda ya nuna aniyarsa ta takarar shugabancin kasar nan, wadansu kuma suna ganin cewa Gwamnan zai yi musanye ne da Sanata Barau Jibrin inda Gwaman zai karbi tikitin Sanata mai wakiltar Kano ta Arewa yayin da shi kuma Barau zai samu tikitin takarar Gwamna.

Sannan ga dan Gwamna Ganduje wato Abba Ganduje yana ta shirye-shiryen samun takarar dan Majalisar Wakilai a mazabar Dawakin Tofa daTofa da Rimin Gado daga hannun dan majalisa mai ci, wato Tijjani Abdulkadir Jobe lamarin da ya janyo rashin jituwa a tsakanin dan majalisar da Gwamnan.

Masu sharhi kan al’amuran siyasa a jihar suna ganin idan har ba a magance wadannan abubuwa cikin sauri ba, abu ne da zai zama share fage ga jam’iyyar adawa ta PDP kan yadda za ta samu damar karbar shugabancin jihar a cikin sauki a zaben shekarar 2023.