✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

2023: Masu son gadar Buhari sun sa harama

Sauran ’yan takarar duk mutanen kirki ne. Amma na yi imani cewa ni ne na fi dacewa, a cewar Tinubu.

A Larabar makon jiya ce tsohon Gwamnan Jihar Legas, Sanata Bola Ahmed Tinubu ya lashe zaben fid-da-gwani na Jam’iyyar APC don tsaya mata takara a zaben badi.

Tinubu ya lashe zaben ne da kuri’a 1,371 a yayin da mai bi masa, tsohon Ministan Sufuri, Mista Rotimi Amaechi ke da kuri’a 316, sai Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo ya zo na uku da 235.

Tun kafin gudanar da zaben, mutum bakwai daga cikin 23 da ke neman tikitin a karkashin jam’yyar, suka janye wa Tinubu.

Kuri’un da sauran ’yan takarar suka samu:

1. Chubuike Rotimi Amaechi, tsohon Ministan Sufuri – 316

2. Farfesa Yemi Osinbajo, Matamakin Shugaban Kasa, – 235

3. Sanata Ahmad Lawan, Shugaban Majalisar Dattawa – 152

4. Yahaya Bello, Gwamnan Jihar Kogi – 47

5. David Umahi, Gwamnan Jihar Ebonyi – 38

6. Ben Ayade, Gwamnan Jiyar Kuros Riba – 37

7. Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Ahmed Sani Yerima – 4

8. Chukwuemeka Nwajiuba, tsohom Minista a Ma’aikatar Ilimi – 1

9. Dokta Ogbonnaya Onu – 1

10. Sanata Rochas Okorocha, tsohon Gwamman Jihar Imo – 0

11. Fasto Tunde Bakare- 0

12. Tien Jack-Rich – 0

13. Abasi Ikoli – 0

Haka kuma a ranar Larabar ce daliget suka tabbatar da takarar Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso a Jam’iyyar NNPP a taron jam’iyyar na kasa da ya gudana a Abuja.

Sai kuma Peter Obi wanda shi ne dan takarar Jam’iyyar Labour Party.

Idan za a iya tunawa a ranar Asabar, 28 ga Mayun bana ne, tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar ya zama dan takarar Shugaban Kasa a Jam’iyyar PDP a zaben 2023, bayan ya kada abokan takararsa a zaben fid-da-gwani.

Fitowarsa a zaben 2023 shi ne karo na shida da ya nemi kujerar Shugaban Kasa, wadda ya faro shekara 30 da suka gabata a 1993.

A cikin manyan ’yan takarar hudu, Peter Obi ne kawai yake tsawaya a karon farko, duk da cewa a zaben 2019, shi ne Mataimakin Atiku Abubakar.

Cikas din da Tinubu zai fuskanta Ana daukar Asiwaju a matsayin daya daga cikin sarakunan karaga masu nada Sarki a Jam’iyyar APC, saboda rawar da ya taka wajen samun nasarar Shugaba Buhari a shekarar 2015 da tasirin da ya yi a Kud maso Yamma, musamman Jihar Legas, inda ya rika samar mata gwamnoni tun daga lokacin da wa’adinsa ya kare.

Sai dai a makon jiya ya yi maganar cewa ba don shi ba, da Shugaba Buhari bai zama Shugaban Kasa ba, wanda ya jawo Fadar Shugaban Kasar ta mayar masa martani cewa miliyoyin mutane ne suka kai Shugaba Buhari matsayin, ba mutum daya be.

Zaben Mataimaki da tikitin Musulmi biyu

An kafa Jam’iyyar APC ce a shekarar 2013 bayan hadewar jam’iyyun CPC da ACN da ANPP da kuma wani bangare na Jam’iyyar APGA da kuma Sabuwar PDP (nPDP).

Wane ne zai zama Mataimakin Tinubu yanzu da ya samu tikitin APC? Wannan ce babbar tambayar da take da wuyar amsawa ga masu tallata takararsa a Arewa da masu adawa da ita.

Kuma shi ma wani shinge ne mai wuyar tsallakewa ga Tinubu don kaiwa ga gaci.

Babban dalilin da ya hana Tinubu zama Mataimakin dan takarar Shugaba Buhari a 2015 shi ne kasancewarsa Musulmi.

Duk wani kokari na ganin hakarsa ta cim ma ruwa abin ya faskara, ganin cewar Buhari Musulmi ne kuma shi ma Tinubu Musulmi ne, hakan ya sa a karshe jigajigan jam’iyyar suka ba shi damar ya kawo Kirista da za su yi tafiyar tare da Buhari. Hakan ne ya kai ga fitowar Farfesa Yemi Osinbajo a matsayin Mataimakin Buhari.

Yanzu ma irn wannan yanayi ya sake tasowa. Jiga-jigan Jam’iyyar APC musamman gwamnoni da suke son zama Mataimakansa Musulmi ne.

“Wannan yana daya daga cikin dalilan da wadansu jiga-jigan jam’iyyar biyu suke adawa da takararsa. To, wa zai dauka? Idan ya zabo Musulmi, zai jawo nakasu ga makomar jam’iyyar a yayin zabe a Arewa.

“Haka idan ya dauki Kirista ba zai je ko’ina ba a Arewa,” inji wani dan jam’iyyar.

Kalubalen rashin lafiya

Haka masu adawa da takarar jagoran Jam’iyyar APC din suna amfani da batun rashin lafiyarsa wajen bata shi. Suna gargadin kada a maimaita irin abin da ya faru da Buhari.

A zangonsa na farko, Shugaba Buhari ya rika zuwa Landan domin neman magani, inda ya shafe watanni a daya daga cikin irin wadannan tafiye-tafiye na jinya.

Tsakanin watan Agusta da Oktoban bara, Tinubu ya tafi Landan, domin kula da lafiyarsa. Yayin da Buhari yake can na wasu kwanaki, Tinubu ya shafe watanni da dama. Har ma Buhari ya ziyarce shi.

Bayan ziyarar Shugaban Kasar ce a gidan Tinubu da ke Duchess Mews, Portland Place, a tsakiyar Landan, sai kuma gidan ya zama wurin da kowa ke kai ziyara, inda yaransa na siyasa da masoyansa da magoya bayansa suka yi ta tururuwar kai masa ziyara.

Duk da cewa abokan Tinubu sun ce ya je an yi masa tiyata ce a gwiwa, wadanda suke adawa da takararsa sun rika bayar da wasu dalilai na daban.

Masu sa ido a kan harkokin siyasa suna nanata bukatar da ke akwai ta tsohon Gwamnan ya fito ya bayyana hakikanin yanayin lafiyarsa.

Daga cikin masu tallata shi, akwai tsohon Gwamnan Jihar Borno, Sanata Kashim Shettima, wanda a wata tattaunawa da manema labarai ya bayyana cewa ba aikin karfi Tinubu zai yi ba, inda ya ce aiki ne na shugabanci da ke bukatar basira da kwarewa, wanda a cewarsa Tinubu yana da su.

Shi ma Sanata Bola Tinubu ya sha fada cewa ba aikin karfi ba ne shugabanci ke bukata, inda ya ce yana duk abin da ake bukata domin jan ragamar kasar nan.

Tarnakin da zai dabaibaye Atiku

Alhaji Atiku, ya yi yunkurin ganin ya hau kujerar har sau biyar, ba tare da samun nasara ba, sannan zai sake nema a badi wadda wadansu ke ganin ita ce damarsa ta karshe.

Atiku, wanda ya tsaya takarar Gwamnan Jihar Adamawa a 1990 da 1997, a 1998, an zabe shi a matsayin Gwamnan Jihar, sai dai kafin a rantsar da shi, sai tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo ya dauke shi a matsayin Mataimakinsa a 1999.

Atiku ya taba fafatawa da Cif MKO Abiola da Ambasada Baba Gana Kingibe a zaben neman tikitin takarar Shugaban Kasa a tsohuwar Jam’iyyar SDP a 1993, akwai tarnaki iri-iri da ake ganin za su kawo masa cikas kan cimma burinsa na samun nasara a zaben na badi.

Karba-karbar shugabanci

Akwai tsammanin cewa mulki zai koma Kudu ne a badi bayan Shugaba Muhammadu Buhari, dan Arewa ya kammala shekara takwas a karagar mulki.

A bara, gwamnoni 17 a karkashin Kungiyar Gwamnonin Kudancin Najeriya (SGF), sun dage cewa dole ne Shugaban Kasa na gaba ya fito daga yankin.

Sun samu goyon bayan wasu kungiyoyi daga yankin da suka hada da Afenifere da Ohanaeze Ndigbo da PanNiger Delta Forum (PANDEF), wadanda suka tabbatar da cewa yin hakan shi ne zai tabbatar da adalci.

Wadansu gwamnoni da jama’a daga Arewa ma sun nuna goyon bayansu ga wannan ra’ayi. Ta yaya Atiku zai shawo kan mutanen Kudancin Najeriya su manta da maganar takara, su daina tunanin karba-karba?

Ta yaya zai sa al’ummar yankin za su zabe shi, duk da cewa ana ganin Atiku na iya samun mafi yawan kuri’u daga Arewa a badi?

Dan takara a koyaushe

Ana kallon Atiku a matsayin dan takara a koyaushe saboda ya dade yana takarar inda ya yi yunkuri sau biyar bai samu nasara ba.

A 1993 Atiku ya nemi takarar Shugaban Kasa a Jam’iyyar SDP, inda MKO Abiola ya kayar da shi a zaben fidda-gwani.

Sannan a zaben 2007 ya tsallake duk wani siradi da Shugaban Kasa na wancan lokaci Obasanjo ya kawo masa, inda ya kaddamar da tsayawarsa takarar Shugaban Kasa a karkashin Jam’iyyar AC a shekarar 2007.

Amma ya sha kaye, bayan marigayi Shugaban Kasa Umaru Musa ’Yar’aduwa na Jam’iyyar PDP ya samu nasara, inda Muhammadu Buhari na Jam’iyyar ANPP ya zo na biyu, Atiku na Jam’iyyar AC ya zo na uku.

Atiku ya sake komawa Jam’iyyar PDP kuma ya fito takara a zaben fid-da-gwani na jam’iyyar, inda ya sha kasa a hannun Shugaba Kasa na wancan lokaci, Dokta Goodluck Jonathan a shekarar 2010.

A shekarar 2014, ya koma Jam’iyyar APC gabanin zaben Shugaban Kasa na 2015, inda ya fafata a zaben fid-da- gwani sai dai ya sha kaye a hannun Buhari.

A shekarar 2017, ya koma PDP kuma ya samu tikitin takarar Shugaban Kasa a jam’iyyar a zaben 2019, inda ya sake shan kaye a hannun Shugaba Buhari.

Masu fashin baki suna ganin ya kamata Atiku ya huta ya mara wa wani baya a cikin harkokin siyasarsu.

Ta yaya Atiku zai iya gamsar da ’yan Najeriya cewa takararsa ta Shugaban Kasa ba burin rayuwa ba ce, soyayya ce ta gaskiya ga kasa da al’umma?

Shekaru

Duk da cewa Atiku bai nuna wata alamar yana fama da wata matsala ta lafiya ba, amma dai shekaru ba jiransa za su yi ba. Idan aka zabi Atiku zai cika shekara 77 a duniya wata shida kafin ranar 29 ga Mayun badi da za a rantsar da su.

Tuhuma kan dukiya

Ana kallon Alhaji Atiku a matsayin daya daga cikin ’yan siyasar kasar nan masu dukiya. Sai dai abin bakin ciki, a Najeriya ana kallon ’yan siyasa a matsayin mahandama.

Wannan ya sa masu sukar tsohon Mataimakin Shugaban Kasar suke tababa da kuma tuhumar tushen dukiyarsa.

Duk da cewa ba a tuhume shi da laifin cin hanci da almundahana ba a gaban kotu, amma ana ganin matsalar cin hanci da almundahana za ta iya zame masa kalubalen da ya kamata ya shirya tsame kansa daga ciki kafin yakin zaben badi.

Masu suka kan yi saurin yin tsokaci kan wasu kalamai marasa dadi da kuma zargin cin hanci da almundahana da tsohon ubangidansa, Obasanjo ya yi masa.

Barazanar Kwankwaso da Peter Obi

Dokta Kabiru Sufi masani ne mai sharhi kan al’amuran yau da kullum. A tattaunawarsa da Aminiya ya ce duk da cewa ’yan takarar Shugaban Kasa da suka fito daga manyan jam’iyyun kasar nan biyu, APC da PDP wato Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da Alhaji Atiku Abubakar suna da karfi a yankunansu, amma akwai kalubale babba a gabansu.

Dokta Sufi ya ce idan aka yi la’akari da tasirin da abokan takararsu da suka fito daga wasu jam’iyyun musamman Jam’iyyar NNPP da Injinya Rabi’u Musa Kwankwaso ke yi wa takara da Jam’iyyar Labour Party da Peter Obi ke yi wa takara za a iya cewa sai sun yi shiri sosai don tunkarar babban zaben.

“Idan muka dauki Jam’iyyar NNPP za mu ga cewa jam’iyya ce da take kara samun tagomashi a Arewa kuma dan takararta shahararre ne a wannan yanki.

“Haka yanki ne da ake samun yawan kuri’u lura da yawan jama’a da yawan kananan hukumomi da ke da shi. Ko a zaben fid-da-gwani mun ga cewa daleget da suka zo daga Arewa sun fi na kowane yanki yawa.

“Haka shi ma Peter Obi dan siyasa ne mai karfi kuma shahararre a yankinsa na Kudu maso Gabas. Kuma yana kan gaba a cikin ’yan takarar da suka fi shahara a kafafen sada zumunta na zamani,” inji shi.

Ya ce, “Wani kalubalen shi ne a baya kowa ya san Jam’iyyar PDP tana samun kuri’u masu yawa daga yankin Ibo. To a yanzu da danta ya fito takara a karkashin wata jam’iyya da ba PDP ba ka ga akwai kalubale ga Jam’iyyar ta PDP.”

A cewarsa idan har wadannan manyan jam’iyyu na APC da PDP ba su yi da gaske ba, to wadannan ’yan takara Rabi’u Kwankwaso da Peter Obi za su iya ba su matsala lura da tasirin da suke da shi a yankunansu.

“Lallai sai wadannan manyan jam’iyyun sun yi aiki tukuru ko sai sun kula da wadannan yankuna sosai a lokacin babban zabe. Idan ba haka ba za su fuskanci matsala,” inji Dokta Sufi.

Dole mu ciyar da Najeriya gaba—Bola Tinubu

A jawabinsa na godiya bayan samun nasarar, dan takarar na APC, ya ce ya zama tilas a yi kokarin samar da kasa dunkulalliya, da za a zauna da juna cikin amince ba tare da bambancin kabila ko addini ba.

A cewarsa, “Ina godiya ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, da Uwargidarsa, A’isha Buhari, da Mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo, da shugabannin majalisa da sauransu.

Ya ce “A makonni baya kadan wasu jaridu sun fara rubuta jana’izar jam’iyyarmu, amma yanzu mun dago da karfinmu. Lallai kai Shugaban APC da sauran shugabannin jam’iyya kun yi kokari sosai wajen kunyatar da masu neman ganin bayan APC.

“Yanzu aiki ne a gabanmu, kuma za mu yi da karfinmu. Mun fada wa PDP ta koma gefe ne bayan wofantar da shekara 16 da ta yi.

“Za mu tabbatar mun samar da dandamalin da yaranmu za su ji dadi nan gaba. Ba za mu bari wani ya mayar da kasarmu baya ba.

“Haka jami’an tsaromu da suke aiki ba dare ba rana wajen kare kasarmu, ina tabbatar muku cewa yanzu ne lokacin da za ku ci moriyar kokarinku.

“Ina yaba wa sauran wadanda suka tsaya takara, ba karamin abu ba ne tsayawa takarar Shugaban Kasa. Kun yi kokari.

“Ina kuma godiya ga wadanda suka janye min. Haka kuma su ma wadanda ba su janye min ba, babu wata matsala ban kullaci kowa a zuciya ba. Ku zo mu hada karfi da karfe mu kayar da PDP.

“Jam’iyyar PDP babu abin da ta kawo face talauci, ta’addanci da karya. Allah Ya albarkaci Najeriya.”

Da yake jawabi kafin fara zaben, Bola Tinubu, ya ce ya zama tilas wadanda suka yi takara da sauran masu ruwa-da-tsaki su hada karfi da karfe domin jam’iyyar ta ci gaba da rike madafun iko bayan 2023.

Ya ce dole ne magajin Shugaba Buhari ya kasance yana da gogewa da himma wajen tafiyar da al’amuran al’adu dabandaban na kasar nan.

Tinubu ya ce tarihinsa na shugabancin kamfanoni da kwarewa a fannin gudanar da kudi da gogewarsa a matsayinsa na Gwamnan Jihar Legas ya ba shi kwarewar da ake bukata don hanzarta sauye-sauyen ci gaba da za su sauya fasalin tattalin arzikin kasa.

“Ina yaba wa sauran ’yan takara bisa martabawa da kishin da suka nuna yayin yakin neman zabe, hakan zai sa jam’iyyarmu ta yi nasara.

“Sauran ’yan takararmu duk mutanen kirki ne. Amma na yi imani cewa ni ne na fi dacewa,” inji shi.

“Ina da gogewa. Na kawo sauyi a Jihar Legas daga wuri mai hadari da ba a yarda da shi ba a 1999 zuwa wuri mai tsafta, aminci, kyau da matsayi na biyar mafi girma na tattalin arziki a duk Afirka.

An sha sukarsa kan bai kamata ya tsaya takara saboda tsufa, ana cewa ya huta, amma a lokuta da dama yakan ce ba zai yi ritaya ba har sai ya mulki Najeriya.

Abin da Buhari ya fada wa daleget a taron APC

A jawabinsa a wajen taron, Shugaba Muhammadu Buhari ya yi kira ga ’ya’yan Jam’iyyar APC su ci gaba da zama a dunkule tare da kauce wa sabani.

Ya ce muhimmin aikin da ke gaban Shugaban APC, Abdullahi Adamu shi ne ya ci gaba da samar da hadin kan ’ya’yan jam’iyyar tare da tabbatar da sasantawar da ake bukata domin maslaharta.

Shugaba Buhari ya bai wa shugaban jam’iyyar da daukacin ’yan Kwamitin Gudanarwar Jam’iyyar (NWC) tabbacin goyon bayansa.

Dangane da al’amuran mulki da yadda gwamnatinsa ta tafiyar da mulkin cikin shekara bakwai da suka gabata, Shugaban ya ce gwamnatin APC duk da cewa ta iske tattalin arzikin ya kusa mutuwa, ta samu ci gaba sosai wajen aiwatar da gyare-gyare da samar da ababen more rayuwa da jin dadin jama’a da kuma ceto Najeriya.

Daleget din Jigawa ya rasu a Abuja

Wani daleget din Jam’iyyar APC daga Jihar Jigawa, Alhaji Isa Baba Buji, ya rasu yayin da yake shirin halartar filin zaben fid-da-gwanin jam’iyyar a Abuja.

Alhaji Isa Buji, wanda ya fito daga Karamar Hukumar Buji a Jihar Jigawa ya rasu ne da safiyar ranar Talata a Abuja.

Kakakin Jam’iyyar APC na Jihar Jigawa, Bashir Kundu ya tabbatar da rasuwar deliget din inda ya ce “Ya rasu a safiyar Talata.”

Rahotanni sun ce marigayin a yanke jiki ya fadi ne a Ofishin Hulda da Jama’a na APC da ke Abuja, lokacin da yake shirin zuwa wurin zaben fid-da-gwanin.

Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya mika sakon ta’aziyya ga ’yan uwan mamacin a shafinsa na Twitter.

Sakon ta’aziyyar da Kakakinsa, Laolu Akande, ya wallafa ya ce, “Mataimakin Shugaban Kasa, Osinbajo ya bayyana damuwarsa da samun labarin rasuwar daya daga cikin daleget din APC daga Karamar Hukumar Buji a Jihar Jigawa, Isa Baba Buji mai shekara 61.

“Yana mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalai, abokai, gwamnati da daukacin al’ummar Jihar Jigawa.”

Kafin rasuwarsa Buji, ya taba zama Mataimakin Shugaban APC na Kudu maso Yamma a Jihar Jigawa.

Rahotanni daga Mudashiru Ismail, da Sagir Kano Saleh da Abiodun Alade da Baba Martins da Abdullateef Salau da Lubabatu I Garba.