✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

2023: Matasan APC sun roki Atiku da Kwankwaso su dawo

Matasan jam’iyyar APC sun roki tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar da tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki da su sake dawowa jam’iyyar. Gamayyar kungiyar…

Matasan jam’iyyar APC sun roki tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar da tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki da su sake dawowa jam’iyyar.

Gamayyar kungiyar matasan ta bukaci Atiku da Sakari da da tsohon gwamann Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da Gwamna Aminu Tambuwal na Sakkwato da Sanata Dino Melaye da sauran kusoshinta da suka sauya sheka da su dawo kafin zaben 2023.

“Muna maraba da dukkan tsoffin ‘yan jam’iyya da suka sauya sheka su duba yiwuwar dawowarsu, domin APC ta gaskiya za ta sake bayyana a babban taron da ke tafe, domin ci gaba da kyawawan ayyukan da ta faro a Najeriya”, inji su.

Shugaban kungiyar matsasan Iliyasu Ibrahim Makinta ya yi kiran ne a Kaduna a lokacin wani taron ‘yan jarida da suka gudanar a ranar Alhamis.

Makinta ya yaba da yadda shugaban rikon APC, Gwamna Mai Mala Buni na Jihar Yobe da ‘yan kwamitinsa ke kokarin dinke barakar da ke cikin jama’iyyar.

Ya ce yadda Buni ya shawo kan kan tsohon Shugaban Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara ya dawo jam’iyyar bayan ya bar ta abun sha’awa ne.

“Muna rokon gwamnoni da dukkannin ‘yan jam’iyya da su tsagaita rikicin domin an ga shaida cewa kwamitin Buni na kokarin damawa da kowa.

Mutanen da ake rokon sun fice daga APC ne bayan rikicin cikin gida da ya kunno kai a jam’iyyar gabanin zaben 2019.

A baya jam’iyyar APC ta yi musu irin wannan kira, bayan dawowar Dogara da da Sanata Barnabas  Gemade daga Jihar Binuwai.

Sai dai Saraki da Atiku sun yi watsi da tayi, ta bakin masu magana da yawunsu, wanda suka ce komawa APC kasada ce, domin jam’iyyar na gab da rushewa.