✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

2023: Mun yi tanadin zuwa zagaye na biyu a zaben Shugaban Kasa

Amma idan ba a yi amfani da su ba, INEC za ta lalata su

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta ce ko da za a bukaci zuwa zagaye na biyu a zaben Shugaban Kasa na 2023, ta tanadi karin takardun kada kuri’a miliyan 93 da za a yi amfani da su.

Shugaban hukumar, Farfesa Mahmud Yakubu ne ya bayyana hakan ranar Juma’a yayin wata tattaunawa da Editocin jaridu a Abuja.

A watan Yulin da ya gabata, wata tawagar Cibiya mai Fafutukar Tabbarar da Dimokuradiyya ta Kasa da Kasa da ke Amurka ta yi hasashen cewa zaben Shugaban Kasa na 2023 zai iya kawo sauye-sauyen da ba a san da su ba a zaben tsarin zaben Najeriya na baya.

Tawagar cibiyar dai ta yi hasashen cewa akwai yiwuwar a karon farko a bukaci zuwa zagaye na biyu a zaben saboda ba lallai ne dan takara ya lashe zaben a tashin farko ba.

Sai dai Farfesa Yakubu, wanda Kwamishinan hukumar mai kuma da wayar da kan masu zabe, Festus Okoye, ya ce INEC za ta buga jimlar takardun kada kuri’a miliyan 187 a zaben na badi.

Ya ambato sashe na 134, karamin sashe na biyu na Dokar Zabe ta Najeriya da ya tanadi zuwa zagaye na biyu tsakanin ’yan takara biyu da ke kan gaba, muddin ba a sami wanda ya lashe shi a karon farko ba.

Ya ce a yanzu haka, jimlar ’yan Najeriya miliyan 93 ne suka yi rajitar zaben, inda aka samu karin masu zabe miyan tara da rabi a kan milyan 84 da ake da su a baya.

“Ya zuwa yau, jam’iyyu 18 ne za su fafata a babban zaben 2023, kuma doka ta tanadi yadda ’yan takara za su fito a zaben saboda yadda doka ta yi tanadi.

“Idan ba a sami wanda ya yi nasara a zagayen farko ba, doka ta tanadi cewa INEC za ta buga sabbin takardun kada kuri’a lokacin da take buga na farko.

“Za mu buga guda miliyan 93 a zagaye na farko, a zagaye na biyun ma haka za mu buga, ko da za a bukaci zuwa zagaye na biyu.

“Idan daga karshe ba a bukaci zuwa zagaye na biyun ba, INEC za ta lalata wadannan kuri’un guda miliyan 93.

“Doka ta ba hukumar kwana 21 ta sake shirya zagaye na biyu, idan bukatar yin hakan,” inji Farfesa Yakubu.