✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

2023: Musulmi Bayerabe muke so ya mulki Najeriya

Babu adalci idan aka bayar da takarar Shugaban Kasa ga Kirista Bayerabe.

Kungiyar Kare Hakkin Musulmi (MURIC), ta ce babu wani dan takara Kirista daga yankin Kudu maso Yamma da zai lashe zaben Shugaban Kasa a 2023.

Kalaman na Daraktan MURIC, Ishaq Akintola, kari ne a kan matsayar kungiyar cewa lallai ne Shugaban Kasar na gaba ya zama Musulmi kuma Bayerabe.

Ya ce matsayar kungiyar ta dogara ne kan matakin jam’iyyun siyasa na fitar da ’yan takarar Shugabancin Kasa  daga yankin Yarbawa.

“Wadansu masu ruwa da tsaki sun yi wa sanarwarmu gurguwar fahimta, cewa muna bukatar  Shugaban Kasa Musulmi kuma Bayarbe a 2023.

“Sun yi mana bahaguwar fahimta cewa ba ma son Shugaban Kasa Kirista kwata-kwata kuma wannan ba daidai ba ne saboda haka lallai ne mu fito mu fayyace matsayarmu.

“Gaskiyar matsayar tamu ita ce muna bukatar Shugaban Kasa na gaba ya zama Bayerabe idan jam’iyyun siyasa sun ba da takarar ga yankin kabilar.

“MURIC ba kungiyar ta’addanci ba ce. Ba mu da matsala in an ce yau Shugaban Kasa Kirista ne; Dimokuradiyya muke yi a Najeriya kuma akwai addinai da dama a kasar.

“Saboda haka ba adawa muke da Kirista ya zama Shugaban Kasa ba muddin dai zai mutunta hakkokin al’ummar Musulmi.

“Mun yi amanna cewa Shugaban Kasa Musulmi kuma Bayarbe zai saurari korafe-korafen Yarbawa Musulmi saboda zai fahimci yadda zamantakewa take a yankin, amma idan Kirista ne to zai kara gasa wa Musulmi Yarbawa aya a hannu.

“Ba wai muna cewa Kiristoci ba za su Shugabanci kasar nan ba ne a 2023, a amma damuwarmu ita ce kar dan takarar ya zama Kirista Bayerabe, saboda dalilai biyu.

“Na farko, Yarbawa Kiristoci ba sa bai wa abokan zamansu Musulmi hakkokin da Allah Ya bai wa dan Adam.

“Akwai misalai da dama ta yadda ake kyarar ’yan mata Musulmi a makarantun Yarbawa, musamman ma kan batun sanya hijabi.

“Sai kuma yadda ba sa barin Musulmi Yarbawa su gudanar da Shari’ar Musulunci wanda ba ta yadda ya shafi Kiristoci.

“Akwai damuwa matuka idan muka zauna karkashin Shugaban da ba ya mutunta hakkokin mutane.

“Na biyu, Yarbawa Kiristoci sun shugabanci kasar nan a lokuta da dama daga Mathew Olusegun Obasanjo (1976–1979, da 1999–2007), da Shugaban rikon kwarya, Earnest Shonekan (Agusta-Nuwamba 1993) da kuma Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, (2015 zuwa yanzu); amma babu Musulmi Bayerabe da ya taba samun damar mulkin kasar nan.

“Don haka, babu adalci idan aka bayar da takarar Shugaban Kasa ga Kirista Bayerabe idan aka bai wa yankin damar fitar da ’yan takara,” inji sanarwar.

A cewarsa, dan takara Kirista daga wata shiyyar ba zai fuskanci adawa ba kamar yadda wanda ya fito daga yankin Yarbawa zai fuskanta.

Ya ce kungiyar ta cimma matsayar ce bisa abin da ta kira yadda aka mayar da al’ummar Musulmi a yankin saniyar ware.

Ya yi zargin cewa Kiristoci sun yi kane-kane a bangaren ilimi a yankin wanda hakan ya haifar da ake cin zarafi da kyarar dalibai Musulmi.

Ya zargi Kiristoci da mamaye harkokin aikin gwamnati sannan suna musguna wa Musulmi a duk lokacin da suka samu dama.