✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

2023: Mutum 13 ke sha’awar gadar Gwamna Tambuwal

Mutanen da ke son cin gajiyar Tambuwal sun fito ne daga cikin jami’iyyun APC da PDP.

Masu sha’awar hawa kujerar Gwamnan Jihar Sakkwato 13 ne ake jin sun fara kunno kai inda ake hasashen daya daga cikinsu zai iya gadar kujerar Gwamnan bayan kammala wa’adin Gwamna Aminu Waziri Tambuwal karo na biyu.

Mutanen da aka sanya wa ido sun fito ne daga cikin jami’iyyun APC da PDP.

A Jam’iyyar PDP wadanda ake jin suna nuna sha’awarsu sun hada da Mataimakin Gwamnan Jihar, Alhaji Mannir Muhammad Dan’iya da Sakataren Gwamnatin Jihar Alhaji Sa’idu Umar da kuma Sanatan Sakkwato ta Kudu Alhaji Abdullahi Danbaba Dambuwa.

Sauran su hada da Kwamishinan Ruwa Alhaji Umar Muhammad Bature da Alhaji Umar Ajiyan Isah da Shugaban Jam’iyyar PDP na Jihar Alhaji Bello Goronyo.

A bangaren Jam’iyyar APC kuma, akwai tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Alhaji Ahmad Aliyu Sokoto da Jakadan Najeriya a kasar Jordan Alhaji Faruku Malami Yabo da Sanata Sakkwato ta Gabas Alhaji Ibrahim Abdullahi Gobir da kuma Alhaji Abdullahi Balarabe Salame sai tsohon Ministan Sufuri Alhaji Yusuf Suleiman da Sanata Abubakar Umar Gada da dan Majalisar Tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Gada da Gwaranyo, Alhaji Musa Sarkin Adar.

Shida daga cikin masu sha’awar tsayawa takarar sun fito ne daga Sakkwato ta Gabas, hudu daga Sakkwato ta Tsakiya sai uku daga Sakkwato ta Kudu.

A yankunan Sakkwato uku kowane yanki ya samar da Gwamna inda Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa ya fito daga Sakkwato ta Gabas, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko daga Sakkwato ta Tsakiya, sai yanzu Gwamna Aminu Waziri Tambuwal daga Sakkwato ta Kudu.

Aminiya ta gano cewa Alhaji Ahmad Aliyu da Ambasada Faruk Malami Yabo da Sanata Ibrahim Gobir a APC su ne suka fi karfi a cikin masu son tsayawa takarar.

A hasashen masu nazarin siyasa da wuyar gaske a ce ba dayansu ne zai yi wa jam’iyyar takara ba domin za su iya samun goyon bayan jagoran Jam’iyyar APC a Jihar Sakkwato, Sanata Aliyu Wamakko domin dukkansu ’yan gidan siyasarsa ne.

A PDP kuma Mataimakin Gwamna da Sakataren Gwamnati a gidan siyasar Tambuwal suke duk da ana zargin Mataimakin Gwamna ya raba kafa hakan ya sanya ake ganin Jarman Sakkwato Alhaji Ummarun Kwabo zai iya goya masa baya.

Kwamared Bello Sambo Bazza, wani mai sharhi ne kan lamuran siyasa a Jihar Sakkwato, ya ce yawaitar masu son tsayawa takarar Gwamnan Jihar Sakkwato alama ce da ke nuna dimokuradiyya ta karfafa a jihar kowa yana son ya ba da tasa gudunmawa duk da akwai wadanda ake ganin kamar ba za su iya ba.

“Abin da ya kamata a yi musamman masu jefa kuri’a su bar daukar lamarin na a yi rai ko a mutu domin ’yan siyasar kansu a hade yake, bai kamata don kana goyon baya ka bari hulda ko dangatakar da ta yi shekara 10 ko 20 ko 30 ta samu matsala ba da dan uwanka ko abokinka,” inji Kwamared din.

Shi kuwa Barista Mu’azu Liman Yabo ya ce “Ya danganci da bigiren da mutane suka samu kansu da tsari irin na siyasa kan tanadin da ya yi ga kujerar Gwamna.

“Ana duba kujerar da alfanun da take da shi, ba don kwarewa da bauta wa jama’a ba, tsarin daga Amurka muka aro shi ko a can za ka samu yawaitar ’yan takara da manufofi daban-daban.

“Tsarin dimokuradiyya da muke yi cike yake da Jari-Hujja, samun yawan ’yan takara abu ne mai kyau in har sun yi wa siyasa fahimta mai kyau ta neman dama don amfanar jama’a.

“Kowa a bari ya kasa kayansa yawan masu nema zabi ne ga wanda zai zaba, samun karancin ’yan takara na sanya a zabi wadanda ba su cancanta ba,” inji Baristan.

Alhaji Malami Muhammad Galadanci tsohon dan Majalisar Dokokin Jihar Sakkwato, kuma jigo a Jam’iyyar APC, ya ce suna jin ana ta fadin akwai ’yan takarar da suke son tsayawa takarar Gwamna a jam’iyyarsu, amma har yanzu ba su bayyana ba domin akwai lokaci, amma ba za ka hana duk mai so ya fara shiri da wuri ba, don hakan zai iya ba ka nasara bisa ga kurarren lokaci.

Kakakin Jam’iyyar PDP a Jihar Sakkwato, Alhaji Yusuf Hausawa ya ce “A jam’iyyance ba mu da labarin ’yan takarar Gwamna domin lokaci bai yi ba, yi wa jama’a aiki a damar da suka ba mu ce a gabanmu ba maganar takarar Gwamna ba.

“Idan lokaci ya yi za a fitar da komai a tsare har zuwa tsayar da dan takara.”