✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

2023: Na fasa takarar Gwamnan Kano a LP, na koma wajen Tinubu – Bashir

Ya ce ya yi watsi da batun takarar tasa, inda zai tallafa wa tafiyar Tinubu

Dan takarar Gwamnan Jihar Kano a jam’iyyar LP, Bashir I. Bashir ya sanar da janyewar daga takarar a hukumance, inda ya ce ya koma APC.

Da yake zantawa da manema labarai a Kano ranar Juma’a, Bashir ya kuma ce ya dauki matakin ne don tallafa wa dan takarar Shugaban Kasa na APC, Bola Tinubu, sannan ya bude ofishin yakin neman zabensa.

A farkon makon nan ne dai aka fara rade-radin dan takarar zai yi watsi da aniyar tasa domin tallafa wa Tinubu, inda tuni jam’iyyar ta ce Allah raka taki gona.

Sai dai a cewar Bashir, “Mun kuma amince za mu yi amfani da kwamitin yakin neman zabenmu wajen nema wa Tinubu kuri’u don ganin ya sami nasarar lashe zaben 2023 ya zama Shugaban Najeriya a 2023.

“Sunan da za a rika kiran tafiyarmu shi ne Dakarun Kawo Canji na Tafiyar Asiwaju da Shettima a 2023,” in ji dan takarar.

Aminiya ta rawaito cewa a ranar Lahadin da ta gabata, Bashir ya tabbatar da ganawarsa da Tinubu a Abuja.

A lokacin dai, hotunan ganawar tasu sun ta yawo a kafafen sada zumunta na zamani, inda aka rika zargin cewa ya koma APC bayan ya yi watsi da kudurin takarar nasa.