✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

2023: Na gamsu da hadin Tinubu da Shettima —Kwankwaso

Na yi farin ciki da wannan hadi na Tinubu da Shettima.

Tsohon gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabi’u Kwankwaso, ya bayyana gamsuwarsa da zabin mataimaki da dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu ya yi.

A Lahadin da ta gabata ce Tinubu ya zabi tsohon gwamnan Jihar Borno kuma Sanatan Borno ta Tsakiya, Kashim Shettima, a matsayin abokin takararsa na Zaben 2023.

Jaridar Punch ta ruwaito Kwankwaso yana bayyana Kashim Shettima a matsayin mutumin kirki wanda ba shi da haufi a kansa.

“Shettima ya kasance takwarana a lokacin da nake gwamnan Kano a wa’adi na biyu. Mutumin kirki ne, mutumin kirki ne. Ina kuma yi masa fatan alheri.

“Na yi farin ciki da wannan hadi [Tinubu da Shettima]; Damuwata kawai ita ce jam’iyyar APC. Don kuwa wannan jam’iyya… ban sani ba dai.

“Bola Tinubu mutum ne mai dabara da tsare-tsare. Na zauna tare da shi sau da yawa da ba zan a iya kirguwa ba daga 1992 zuwa yanzu.

“Zan so na sake zama da shi don na tambaye shi abin da zai yi wanda zai bambanta da abin da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yake yi a yau. Wannan ita ce babbar damuwata gare shi,” in ji Kwankwaso.

Kwankwaso mai shekaru 65, shi ne dan takarar Shugaban Kasa a jam’iyyar NNPP, kuma tsohon Ministan Tsaro a zamanin gwamnatin Shugaba Kasa Olusegun Obasanjo.