✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

2023: Na rungumi kaddara kan hukuncin kotu na hana ni takara – Ahmed Lawan

Ya ce ya rungumi kaddara, ba zai daukaka kara ba

Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmed Lawan ya ce ba zai daukaka kara kan hukuncin da kotu ta yanke kan zaben Sanatan Yobe ta Arewa ba a jam’iyyar APC, inda ta dakatar da shi daga shiga zaben.

A ranar Laraba ce dai Babbar Kotun Tarayya da ke Damaturu, babban birnin a jihar Yobe, inda ta maye gurbinsa da Bashir Machina.

Lawan ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu kuma ya fitar a ranar Alhamis, inda ya ce ya amince da hukuncin da kotun ta yanke na hana shi takara da kuma shiga zaben.

Sanarwar mai taken: “Hukuncin kotu kan takarar Sanatan Yobe ta Arewa”, ta ce, “A [jiya] Laraba, 28 ga watan Satumban 2022, Babbar Kotun Tarayya da ke Damaturu ta yanke hukunci kan wanda ya cancanta ya tsaya takarar Sanatan Yobe ta Arewa a zaben 2023 a jam’iyyar APC.

“Hukuncin da aka ce ya hana ni tsayawa takara. Don haka, na aminta da wannan hukunci na kotu .

“Bayan tuntubar juna da abokaina na siyasa da magoya bayana da masu ruwa da tsaki a mazabata, na yanke shawarar ba zan daukaka kara kan hukuncin ba, na amince da shi.

“A halin da ake ciki, ina ganin ya dace in gode wa mai girma Sanata Ibrahim Gaidam bisa rawar da ya taka a siyasar jam’iyyar APC a jihar Yobe, ina kuma gode wa mai girma Gwamna Mai Mala Buni bisa goyon baya da ‘yan uwantaka da ya nuna min.”

“Ga ‘yan mazabata, ina gode muku baki daya bisa goyon baya, biyayya da sadaukarwar da kuka yi na gina al’ummarmu da kuma gundumar Yobe ta Arewa da kuma jihar Yobe baki daya.

“Ina so in tabbatar muku cewa zan ci gaba da yi muku hidima a kashin kaina da kuma kowane irin aiki a kowane lokaci.

“Mun yi tafiya tare tsawon lokaci, kuma wannan tafiya za ta ci gaba da zama doguwar tafiya mai tsawo, dangantaka ce mai ban sha’awa kuma ba za ta iya katsewa ba idan Allah ya so. Ina kuma tare da ku a kowane lokaci, Alhamdulillah,” inji Sanata Ahmed Lawan.

Shugaban Majalisar ta Dattawa dai ya yi biyu-babu ne a takarar bayan ya tafi takarar Shugaban Kasa bai sayi fom din takarar Sanatan ba, har aka kammala zaben, wanda aka bayyana Bashir Machina a matsayin wanda ya lashe shi.

Sai dai duk wani yunkurin neman Machinan ya janye masa, ya ci tura, sai da kotu ta yanke hukunci a kai.