✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

2023: Rashin su Wike ba zai hana mu cin zabe ba – Hadimin Atiku

Hadimin dan takarar Shugaban Kasar na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, bangaren yada labarai, Phrank Sha’ibu ya ce ko ba kuri’un Gwamnonin G-5 za su iya…

Hadimin dan takarar Shugaban Kasar na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, bangaren yada labarai, Phrank Sha’ibu ya ce ko ba kuri’un Gwamnonin G-5 za su iya lashe zaben 2023.

Sha’ibu ya bayyana hakan ne a wata hira da ya gudanar a wani gidan Talabijin mai zaman kansa a Najeriya, inda ya ce batun da jagoran  Gwamnonin da ke kiransu G-5 ke yi cewa kofar sulhu tsakaninsu da Atiku ta kusa rufewa, sam bai dame su ba.

“Tawagar yakin neman zabenmu ta ajiye wannan batu a gefe. Dama kuma mun fada tun a farko cewa  mu don Najeriya muke yi ba PDP kadai ba.

“Atiku ba shi da wata matsala ta radin kai tsakaninsa da Wike. Amma sai nake karantawa a jarida cewa Wike ya ce sun kusa rufe kofar sulhu da shi.

“To ko sun rufe kofar ai tagar a bude take, kuma Atiku dan siyasa ne ba mai laifi ba. Kuma ba ta tagar ya shiga siyasar ba, ta kofa ya shiga.

“Sannan Gwamna Wike mutum guda ne, mai kuri’a daya, haka ma sauran Gwamnoni hudu na G-5,” in ji shi.