2023: Tinubu ya amince zai dauki Musulmi abokin takara —Ganduje | Aminiya

2023: Tinubu ya amince zai dauki Musulmi abokin takara —Ganduje

Tinubu da Ganduje
Tinubu da Ganduje
    Ishaq Isma’il Musa da Usman Bello Balarabe, Kano

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano, ya ce dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya amince zai dauki Musulmi a matsayin abokin takararsa.

Ganduje ya bayyana haka ne a yayin wata ziyara da manyan malaman jihar kusan 100 suka kai masa ranar Juma’a a gidan gwamnatin jihar.

Ganduje ya ce “Mun ba shi shawara ya dauki Musulmi a matsayin mataimaki kuma ya amince, saboda ba wani abu ba ne sabo a Najeriya.”

Ya kuma yi kira ga taron malaman da su rika yi wa Tinubu addu’o’in samun nasara a zaben 2023.

A yayin da ya mika kokon barar addu’o’in samun zaman lafiya da ci gaba a Jihar Kano, Ganduje ya kuma bukaci malaman da su yi wa mataimakinsa kuma dan takarar gwamnan Kano na jamiyyar APC a zaben 2023, Yusuf Gawuna addu’ar samun nasara.