✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

2023: Tsohon Gwamnan Yobe ya lashe zaben fid da gwanin Sanata a APC

Ya lashe zaben ne babu hamayya

Tsohon Gwamnan Jihar Yobe, Ibrahim Gaidam, ya sake lashe zaben fid da gwanin jam’iyyar APC don wakiltar mazabarsa ta Yobe ta Gabas.

APC dai ta gudanar da zaben ne ba tare da hamayya ba don fitar da dan takarar da zai yi wa jam’iyyar takara a zaben 2023 mai zuwa.

Wakilan jam’iyyar APC na mazabar sun sake zabar tsohon Gwamnan baki daya a zaben fid da gwanin da aka gudanar a Damaturu, babban birnin Jihar kwanan nan.

Sanata Gaidam ya yaba wa wakilan da suka sake zabar sa a zaben na fidda gwani don sake wakiltar shiyyar a mataki na gaba.

Ya kuma ba wa al’ummar mazabar tasa  tabbacin samun wakilci mai ma’ana domin samun karin romon Dimokuradiyya ga shiyyar da Jihar baki daya.