✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

2023: Yadda za ta kaya a zaben shugaban kasa

Baya ga shugaban kasa, ’yan Najeriya za su zabi ’yan Majalisar Wakilia 360 da kuma sanatoci 109

A yau asabar ’yan Najeriya miliyan 87 masu katin zabe za su fita rumufunan zabe domin kada kuri’ar zaben shugaban da zai jagoranci kasar na shekara hudu.

Baya ga shugaban kasa, ’yan kasar mai yawan al’umma sama da 200 za su zabi ’yan Majalisar Wakilia 360 da kuma sanatoci 109 a zaben na ranar Asabar.

Za a gudanar da zabukan ne a mazabu 1,491 da ke kananan hukumomi 774 da ke jimillar rumufunan zabe 176, 846 a kasar mai jihohi 36 da kuma Babban Birnin Tarayya, Abuja.

Alkaluman da INEC ta fitar sun nuna kasarin ’yan kasar da za su yi alkalanci a zaben matasa ne, masu shekara 18 zuwa 35.

Duk wanda ya yi nasara a matsayin zababben shugaban kasa, zai karbi ragamar jagoranci daga hannun Shugaba mai ci, Muhammadu Buhari a ranar 29 ga watan Mayu  2023 zuwa ranar 29 ga Mayun 2027.

Wanna shi ne babban zabe na bakwai ke nan da ’yan kasar za su zabi shugaban kasa da ’yan Majalisun Tarayya, tun bayan dawowar Najeriya kan tsarin dimokuradiyya a shekarar 1999.

Jam’iyyu 18 ne za su fafata a zaben da za a gudanar a kasar mai yawan al’umma sama da miliyan 200, wadda ita ce kasa mafi yawan al’umma a nahiyar Afirka.

Masu bibiyar harkokin zabe na hasashen shugaban kasar Najeriya na gaba zai fito ne daga daya daga cikin manyan jam’iyyu hudu — APC, LP, NNPP da PDP.

APC ita ce jam’iyya mai mulkin kasar tun a shekarar 2015 karkashin Shugaba JMuhammadu Buhari, ta tsayar da uban jam’iyyar na kasa, Bola Tinubu, wanda dan kasuwa ne kuma tsohon sanata kuma tsohon Gwamnan Jihar Legas na tsawon shekara takwas.

LP ta tsayar da attijiri kuma tsohon Gwamnan Jihar Anambra, kuma tsohon dan takarar mataimakin shugaban kasa a PDP a zaben 2019.

Fitowarsa takara a LP a wannan karon ya ba wa jam’iyyar da karfi a matakin zaben shugaban kasa a karon farko, sabanin shekarun baya da jam’iyyar ke shahun baya.

NNPP kuwa, dan takararta shi ne tsohun Kano a karo biyu, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, wanda tsohon ministan tsaro ne kuma tsohon mai neman takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC a 2015.

Babbar jam’iyyar adawa ta PDP kuwa, dan takararta shi ne tsohon shugaban kasa na shekara takwas (1999-2007), wanda karo na shida ke nan da yake zawarcin kujerar shugaban kasa.