✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

2023: Yarima ya bayyana kudirin tsayawa takara

Kuna dai ganin yadda a yanzu ake fuskantar kalubale da dama musamman a fannin sha’anin tsaro.

Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Sanata Ahmad Sani Yarima, ya bayyana kudirin tsayawa takarar shugabancin Najeriya karkashin inuwar jami’iyyar APC a babban zaben kasa na 2023.

Sanata Yarima wanda ya wakilci Zamfara ta Yamma a Majalisar Dattawa daga shekarar 2007 zuwa 2019, ya bayyana aniyarsa ne yayin zanta wa da manema labarai ranar Laraba a birnin Abuja.

Tsohon gwamnan cikin bayyana azamar samun nasara, ya ce ya yanke shawarar tsayawa takara ne don inganta rayuwar ’yan Najeriya tare bayyana damuwa kan yadda kashe-kashe da zaubar jinin al’umma ya zamto ruwan dare a fadin kasar.

Kazalika tsohon gwamnan yayin hirarsa da manema labarai, ya koka da yadda talauci ya yiwa kasar nan katutu, yana mai cewa ya kamata a magance lamari cikin gaggawa.

“Za ku iya tuna cewa a shekarar 2006, na bayyana ra’ayi tsayawa takarar Shugaban Kasa bayan na yi wa jihar Zamfara aiki a matsayin gwamna na tsawon shekaru takwas.”

“Sai dai daga baya na janye kudirin takarar Shugaban Kasa kuma tun daga wancan lokacin na tafi Majalisar Dattawa wanda inda na yi wa’adi har uku.”

“A yanzu da Shugaba Buhari yake kammala wa’adinsa na biyu, na yanke shawarar sake gwada sa’a ta don ganin yadda Allah zai yi a yayin da na yanke shawarar ba zan sake koma wa Majalisar Dattawa ba.”

“Kuna dai gani a yanzu Najeriya na fuskantar kalubale da dama musamman a fannin sha’anin tsaro amma a matsayina na daya cikin jiga-jigan jam’iyyar APC, ina da dama a koyaushe na gana da Shugaban Kasa kuma in bada tawa shawarar don har yanzu ina ganin za a iya shawo kan wadannan kalubalen ta hanyar hadin kai.”

Yarima ya ce ya kirkiro wata manhaja don tabbatar da cewa kafin ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takara a hukumance, zai samu akalla magoya baya miliyan 30 zuwa 40.