✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

2023: Zaman Atiku dan takarar PDP ya rikita APC

Zaman Atiku dan takarar shugaban kasa na babban jam’iyyar adawa ta PDP ya dagula wa jam’iyyar APC mai mulki lissafi.

Zaman Atiku dan takarar shugaban kasa na babban jam’iyyar adawa ta PDP ya dagula wa jam’iyyar APC mai mulki lissafi.

Aminiya ta gano cewa bayan nasarar Atiku a zaben fid-da-gwanin PDP, shugabannin APC suka fara lissafin zabin da ya rage musu cikin abubuwa biyu wajen fitar da dan takarar shugaban kasar jam’iyyarsu.

A hannu guda kuma, majiyoyi masu tushe a PDP sun ce tuni Atiku ya fara neman wanda zai kasance mishi dan takarar mataimakin shugaban kasa a zaben na 2023.

Wani jigo a bangaren Atiku ya ce Atiku na duba yiwuwar daukar wani gwamna mai ci daga yankin Kudu maso Yamma a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa.

PDP dai ta yi watanni tana kwan-gaba-kwan-baya kan karba-karbar takarar shugaban kasa tare da dage babban taronta na zaben dan takarar sau biyu.

A karshe dai ta gudanar da zabenta na dan takarar shugaban kasa a ranar Asabar, wanda Atiku daga yankin Arewa ya lashe.

A ranar Juma’a, Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) dai ta dora wa PDP da janyo kara wa’adin farko da ta hukumar ta sanya na ranar 3 ga watan Yuni, 2022 domin kammala zabukan fid-da-gwanin jam’iyyu gabanin zabukan 2023.

APC ta shiga lalube

Duk da cewa kwana bakwai ya rage APC ta yi nata zaben fid-da dan takarar shugaban kasa, amma Aminiya ta gano kawo yanzu babu wani kwakkwaran motsi da jam’iyyar ta fara game da taron.

Jagorori da masu neman takara da sauran masu ruwa da tsaki a jam’iyyar sun samu rabuwar kai game da abin da za su yi. 

Uwa uba, an dage ranar da aka sanya na tantance mutum 23 da ke neman takarar shugaban kasar da aka shirya gudanarwa ranar Litinin da ta gabata, har sai abin da hali ya yi.

Ga shi kuma Kwamitin Gudanarwar Jam’iyyar (NWC) wanda tsohon Gwamnan Jihar Nasarawa, Sanata Abdullahi Adamu, bai nada kwamitin da zai yi aikin ba, ballantana sanya sabon ranar da za a yi tantancewar ba.

Daga cikin mutum 23 da ke neman tikitin takarar shugaban kasa a jam’iyyar, masu ruwa da tsaki sun fi karkata kan Uban Jami’iyyar na Kasa, Bola Ahmed Tinubu; Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo; Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan da kuma tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi. 

Zabin da ke gaban APC

Majiyoyi a jami’iyyar dai sun shaida wa wakilanmu cewa jam’iyyar na duba yiwuwar daya daga cikin abubuwa biyu.

“Ko ta yi shakulatun bangaro da yankin Kudu, ta dauko dan Arewa; ko kuma a bar  abin a bude, a jira duk sakamakon da hakan zai fitar,” inji wata majiyarmu a jam’iyyar.

A kwanakin baya Aminiya ta yi wani rahoto na musamman kan yadda ake cuku-cukun ganin jam’iyyar ta sake tsayar da dan Arewa takarar shugaban kasa a zaben 2023.

Yanzu da Atiku ya zama dan takarar PDP, batun na kara kwari a APC; Amma wasu kusoshin jam’iyyar a Abuja na kokarin ganin tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya zama dan takarar shugaban kasar jam’iyyar.

’Yan Arewa da ke zawarcin tikitin a APC su ne;  Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan; Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello; Gwamnan Jihar, Mohammed Badaru Abubakar da tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Sanata Ahmed Yarima. 

Wani tsohon gwamna dai ya saida wa wakilinmu cewa nasarar Atiku a zaben dan takarar PDP ya sauya musu lissafi.

Ya ce: “In banda wasu ’yan baranda a Villa da ke amfani da sunan Buhari cewa ya amince da Amaechi, fitowar Atiku ya sauya alkiblar gaba daya.

“In ba Tinubu ba, akwai wanda zai iya karawa da Atiku a fadin kasar nan kuma ya maimaita irin nasarar da Abiola ya samu inda ya doke marigayi Bashir Othman Tofa a Kano?

“Tabbas Atiku yana da yawan kuri’un Arewa, amma Kwankwaso zai kwashi kuri’u daga Arewa maso Yamma. 

“Don haka dole sai dan takara nagari daga Arewa ne zai yi iya gogayya da shi, kuma mishi illa a yankinsa na Arewa maso Gabas shi ne abin yi,” inij shi.

Amma kuma, a ranar Lahadi, tsohon Gwamnan Jihar Abia, Sanata Orji Uzor Kalu, ya ce nasarar Atiku a PDP ya rufe kofar samun dan takarar shugaban kasa daga yankin Kudu a APC.

Kalu, wanda shi ne Mai Tsawatarwar Majalisar Dattawa kuma daya daga cikin masu tallata takarar Shugaban Majalisar, Sanata Ahmad Lawan, ya bukaci Buhari ya bayyana wanda yake so ya gaje shi a jam’iyyar.

Kudu su hakuwa kawai —Orji Kalu

“A jam’iyyarmu, yanzu babu yadda za a yi a kawo maganar dan takara daga yankin Kudu, idan ba so APC take yi a yi mata ritaya a siyasa,” inji Sanata Orji Kalu.

Don haka ya bukaci APC ta bai wa yankin Arewa maso Gabas takarar shugaban kasa.

“Ina rokon Shugaba Buhari ya zabi magajinsa daga yankin Arewa maso Gabas, wannan shi ne adalci ga yankin.

“Idan aka bai wa Arewa maso Gabas, kadan zai rage a yankunan da ba su yi shugaban kasa ba,” inji sanarwar da ya fitar.

Tinubu ne daidai da Atiku —Talban Bauchi

Amma Talban Bauchi, Tahir Ibrahim Tahir, a cikin wata makala ya ce, Tinubu ne kadai dan takarar da zai iya gogayya da Atiku. 

“Wajibi ne APC ta mutunta yarjejeniyar da ta yi na karba-karba, duk da cewa ba a rubuce ba ne, domin dacewa da tsarin federaliyya.

“A matsayin Tinubu na dan yankin Kudu, shi ne kadai dan takarar da ya nuna yana damawa da kowa, kamar dan Arewa,” inji shi.

Yanzu lokacinmu ne —Kudu maso Yamma

Gamwayyar jagororin APC na yankin Kudu maso Yamma sun yi kira ga Shugaba Buhari kada ya saba yarjejeniya da alkawarin da shugabannin jam’iyyar suka yi gabanin zaben  2015. 

Sanarwar da shugabansu, Fatai Bola Adekunle, ya fitar ta ce wajibin Buhari ne ya tabbata dan yankin Kudu maso Yamma ne ya zama magajinsa a 2023. 

Adekunle ya ce yin sabanin hakan ba komai ba ne face cin amana daga Shugaba Buhari da mukarrabansa ga yankin Kudu maso Yamma da suka yi uwa, suka yi makarbiya wajen ganin ya zama shugaban kasa a 2015. 

“Muna kira ga Buhari da ya mai da biki da abin da yankin ya yi mishi a 2015 ta hanyar tabbatar da ganin dan yankinmu ya gaje shi a 2023 a matsayin saka mana irin alherin da muka yi mishi. 

“Kowa shaida ne kan irin rawar da muka taka don ganin ya ci zabe kuma sanin kowa ne cewa ba don yankin Kudu maso Yamma da Arewa sun hade ba, to da Buhari bai zama shugaban kasa ba”, inji su. 

Sun kuma yi kashedi game da rade-radin da ake yi cewa ana kokarin bai wa Jonathan tikitin takarar.

Ina ruwan Buhari da Jonathan?

Amma da wakilinmu ya tuntubi wani hadimin Buhari, ya shaida mishi cewa babu ruwan shugaban kasar a kokarin ganin Jonathan ya tsaya takara a APC. 

Ya ce a ranar Lahadi an bayar da umarci cewa daga yanzu kada a fitar da hotunan duk wata ganawa tsakanin Buhari da Jonathan, domin kada a dauki hotunan ganawar a matsayin alamar goyon bayan Jonathan.

Wakilanmu sun gano cewa Fadar Shugaban Kasa ta damu ne ganin yadda hadiman Jonathan suke amfani da hotunan ziyarar da ya kai wa “Shugaban APC na Kasa, Abudllahi Adamu da kuma Alhaji Mamman Daura, wajen nuna cewa suna tare da shi”.

Daga Sagir Kano Saleh, Ismail Mudashir, Itodo D. Sule & Muideen Olaniyi